Dan adam da kudi: Yadda wani ya mayarwa banki kudin da aka turo masa bisa kuskure

Dan adam da kudi: Yadda wani ya mayarwa banki kudin da aka turo masa bisa kuskure

  • Stephen Waiganjo ya zama abin fade a garin Eldama Ravine bayan dawo da kudaden da yawamsi ya kai N365k da aka tura asusunsa bisa kuskure
  • Waiganjo ya jira banki su zare kudin amma ba su yi hakan ba, wanda hakan ya sa ya yi tattaki zuwa bankin domin fada masu abin da ya faru
  • Bankin ya sami damar cire kudin daga asusunsa bayan haka ya tura kudin zuwa ga asusun da ya dace

A ranar 27 ga Janairu, 2022, da misalin karfe 10 na safe, aka turo wa Stephen Waiganjo kudi KSh 100,000 (N365k) cikin asusunsa na M-Pesa daga bankin NCBA na Nairobi.

Ganin cewa bai yi tsammanin wannan adadin kudi daga kowa ba, sai ya ci gaba da gudanar da harkokinsa yana jiran mai kudin ya nemi hakkinsa.

Kara karanta wannan

Ahmad Musa ya yiwa tsohon dan kwallon da ya talauce kyautar N2m

Mutumin kirki ya mayar da kudin da aka tura masa bisa kuskure
Dan adam da kudi: Yadda wani ya mayarwa banki kudin da aka turo masa bisa kuskure | Hoto: Baringo
Asali: Facebook

Ya bayyana a cikin wata hira da aka yi dashi yadda ya nemi a mai da kudin ga mai su amma ya gagar, wannan yasa ya tafi banki.

Ya dawo da kudin da ba nasa ba

Mutumin mai shekaru 40 daga kauyen Shauri Yako da ke garin Eldama Ravine ya yi tattaki zuwa bankin NCBA da ke Nakuru inda ya bayyana kuskuren da aka yi na turo masa kudin.

Bayan sauraro da fahimtar batunsa, an ba da izinin a mayar da kudin ga mai su.

Lamura sun bayyana cewa mutumin da ya turo kudin ya shigar da lambar wayar Waiganjo cikin tsarin biyan kudi bisa kuskure.

Mahukuntan bankin sun yabawa Waiganjo, wanda ma’aikacin wucin gadi ne a Asibitin Eldama Ravine Sub-County, bisa gaskiya da amanarsa.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Kwamitin bincike ya bukaci a rage wa Abba Kyari matsayi zuwa ACP

"Mutane ka iya zama talakawa a fili, amma masu arziki a zuci," in ji wakilin abokan cinikayya, Ms Sharon Chelagat game da labarin Waigango.

Dare daya: Yadda dan crypto ya zama miloniya a wata sabuwar duniyar crypto wai ita NFT

A wani labarin, Daniel Maegaard a da yana samun Naira 6,500 kacal a kowane awa idan ya yi aiki a wani gidan mai a karshen mako yayin da yake karatun ilimin halayyar dan adam a wata Jami'ar.

Maegaard ya kasance yana tara kwabban crypto yayin da yake hada aikinsa da karatu amma gogewa a fannin fasaha da sa'ar rayuwa sun sa ya zama hamshakin attajirin dare daya.

Ya yi tuntube da wani tsagin duniyar crypto da ake kira Non Fungible Tokens (NFTs) shekaru kafin su zama abin da suke yanzu. Wannan ya ba shi damar zama miloniya a cikin shekaru goma da suka gabata.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel