Abokanan Juna 4 sun lakaɗawa abokinsu duka har ya mutu kan zargin ya saci waya, Daga baya anga wayar

Abokanan Juna 4 sun lakaɗawa abokinsu duka har ya mutu kan zargin ya saci waya, Daga baya anga wayar

  • An gurfanar da wasu abokanai hudu a gaban alkalin kotun Majistire dake Yola bisa zargin azabtar da wani matashi da duka har ya mutu
  • Rahoto ya nuna cewa sun halaka mutumin ne bisa zargin ya saci wayar ɗaya, amma daga baya an gano wayar ba shi ya ɗauka ba
  • Yanzun haka mutum biyu sun shiga hannu, yayin da ake cigaba da neman sauran, bayan mutuwar matashin

Yola. jahar Adamawa - An gurfanar da wasu abokan juna 4 a gaban Kotun Majistire dake Yola, bisa zargin kashe Adamu Ahmad, ɗan shekara 28, wanda suka yi zaton ya saci wayar salula.

Punch ta rahoto cewa ɗan Magajin garin Damare da aka tsige, Hamidu Umar, ya zargi mamacin da sace masa waya ranar 22 ga watan Janairu, a karamar hukumar Yola ta kudu.

Duk da cewa mamacin ya musanta zargin ɗaukar wayar, amma Umar ya nace ya zama wajibi ya fito masa da wayarsa.

Taswirar jahar Adamawa
Abokanan Juna 4 sun lakaɗawa abokin duka har ya mutu kan zargin ya saci waya, Daga baya anga wayar Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Rahotanni sun bayyana cewa Umar da kuma wasu abokanansa uku sun azabtar da mutumin domin tilasta masa ya amsa cewa ya ɗauki wayan.

Umar da taimakon abokansa, suka ɗauki mutumin zuwa wani kangon gini da ba'a kammala ba da yamma, suka azabtar da shi da dukan icce da bulo.

Ahmadu, ya samu karaya a baki ɗaya hannuwan sa biyu sanadin wannan azabtarwan da wasu raunuka, wanda ya yi sanadin mutuwarsa.

Shin sun amsa laifinsu a gaban Kotu?

Yayin da aka gurfanar da su, Umar ya kara jaddada cewa ba shi da hannu a lamarin, yayin da abokinsa na biyu, Manas ya amince da laifin.

Manas ya shaida wa Kotu cewa sun haɗu da Umar da sauran mutum biyu, suka yi wa mamacin Dukan tsiya, kuma duk Umar ne ya umarce su da yin haka.

Shin ina aka gano wayar?

Bayanai sun bayyana cewa sabon shugaban gundumar Damare, Sahabo Umar shine ya kubutar da wanda ake zargi na farko, kuma ya sake kai ƙorafi Caji Ofis ɗin Wuro Hausa.

"Bayan dawowar Umar gida, ya tarad da wayar da yake tsammanin an ɗauke masa a kan kujerun dake Falon sa."

Rahoto ya nuna cewa mutumin da suke zargi ya ɗauki wayar, wanda suka lakadawa dukan kawo wuka ya rasu a cibiyar lafiya ta tarayya, Yola, kuma tuni aka masa jana'iza.

A wani labarin na daban kuma Gwamna ya shirya tattaunawa da kungiyoyin dake aikata ta'addanci a jiharsa

Gwamnatin jihar Oyo ta fara shirin tattaunawa da kungiyoyin da basa ga maciji domin dakile kashe-kashe a faɗin jihar.

Kwamishinan labarai da wuraren buɗe ido, Wasiu Olatunbosun, ya ce bayan haka duk kungiyar da ta cigaba zata ɗanɗana kuɗarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel