Duk Jirgi ɗaya ya kwaso mu, Dattawan Arewa sun gana da tsohon shugaban ƙasa Obasanjo

Duk Jirgi ɗaya ya kwaso mu, Dattawan Arewa sun gana da tsohon shugaban ƙasa Obasanjo

  • Shugaban ƙungiyar dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi, da wasu manyan yan tawagarsa sun gana da Obasanjo a Ogun
  • Abdullahi ya bayyana cewa sun tattauna batutuwa masu muhimmanci game da ƙasar nan yayin da zaɓe ke ƙara kusantowa
  • Ya ce da kungiyarsu ta dattawan arewa da su Obasanjo duk a shafi ɗaya suke kuma manufarsu ɗaya

Ogun - Shugaban ƙungiyar dattawan arewa, (NEF), Ango Abdullahi, ya ce akwai bukatar amfani da dabaru domin gyara Najeriya, yayin da zaben 2023 ke ƙaratowa.

The Cable ta ruwaito cewa Abdullahi ya yi wannan furucin ne bayan gana wa da tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, a Abeokuta, jihar Ogun.

A cewar hadimin Obasanjo, Kehinde Akinyemi, Abdullahi ya samu rakiyar shugaban kwamitin amintattu na kungiyar CNG, Nastura Shariff, da kuma Daraktan ayyuka, Aminu Adamu.

Kara karanta wannan

Kotu ta sa a yi wa matashin ɗan kasuwa Bulala Bakwai a jihar Kaduna

Dattawan Arewa da Obasanjo
Duk Jirgi ɗaya ya kwaso mu, Dattawan Arewa sun gana da tsohon shugaban ƙasa Obasanjo Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Farfesa Abdullahi ya bayyana cewa duk da shekaru sun ja, amma har yanzun za su iya ba da gudummuwa ga al'umma da ƙasa baki ɗaya.

Daily Trust ta rahoto Ya ce:

"Bana son yin nesa da shi na tsawon watanni ko shekaru ban ganshi ba, musamman a irin wannan lokacin. Saboda haka na kawo masa ziyara ne dan mu gaisa kuma ya mana bayanin hangensa a kan ƙasa."
"Mu ma mun ba shi bayanin yadda ƙasa ke ciki, mun sanya wasu abubuwa a Sikeli kuma mun cimma matsaya a kan wasu batutuwa."

Me suka tattauna?

Da aka tambayesa ko kungiyarsu tana tare da kungiyar waɗan da suka tarbe su, Farfesan ya ce:

"Eh, duk muna tare a shafi ɗaya, kuma Insha Allahu hakan zai zama Alheri. Muna cikin ƙalubale da yawa kuma kullum maganar mu kan abu ɗaya."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari ya soke taronsa da gwamnonin APC bayan sun hallara, zai shilla turai

"Ku manema labarai ne, kun san abin da muka jima muna faɗa a kan halin da ƙasar nan ke ciki. Abubuwa sun lalace, zaɓe na ƙara kusantowa. muna fatan mu yi shiri me kyau dan goben ƙasar mu."

Shugaban NEF na ɗaya daga cikin waɗan da ke goyom bayan canza ɗabi'un yan ta'addan da suka miƙa wuya.

Ya shawarci gwamnatin tarayya ta yafe wa yan bindiga laifukan su kamar yadda a baya ta yafe wa mayakan Neja Delta.

A wani labarin na daban kuma Buhari ya ɗage ganawarsa da gwamnonin APC bayan sun hallara

Shugaba Buhari ya soke ganawar da aka shirya zai yi da gwamnonin jam'iyyarsa ta APC a fadarsa Aso Villa, dake babban birnin tarayya Abuja.

Tuni dai wasu gwamnonin suka samu hallara domin gudanar da taron, yayin da shugaban ke shirin kama hanya zuwa Turai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel