Gwamna ya shirya tattaunawa da kungiyoyin dake aikata ta'addanci a jiharsa

Gwamna ya shirya tattaunawa da kungiyoyin dake aikata ta'addanci a jiharsa

  • Gwamnatin jihar Oyo ta fara shirin tattaunawa da kungiyoyin da basa ga maciji domin dakile kashe-kashe a faɗin jihar
  • Kwamishinan labarai da wuraren buɗe ido, Wasiu Olatunbosun, ya ce bayan haka duk kungiyar da ta cigaba zata ɗanɗana kuɗarta
  • Ya ce a halin yanzun zasu haɗa hannu da hukumomin tsaro da Yan sa'kai wajen warware matsalolin kungiyoyin

Oyo - Gwamnatin jihar Oyo karkashin jagorancin gwamna Seyi Makinde, zata tattauna da kungiyoyin yan daban Anguwa da na yan asiri domin dawo da zaman lafiya.

Daily Trust ta rahoto cewa waɗan nan ƙungiyoyin na yan daba da yan asiri, sune suka hana zaman lafiya a jihar Oyo ta hanyar kashe-kashen al'umma.

Kwamishinan labaru da wuraren bude ido, Dakta Wasiu Olatunbosun, shi ne ya bayyana shirin da gwamnati ke yi bayan gana wa da shugabannin jami'an tsaron wasu ƙungiyoyi.

Kara karanta wannan

Mu ma nan ba da dadewa ba da yiwuwan mu shiga yajin aiki, Kungiyar Malaman Poly ASUP

Gwamnan Oyo, Seyi Makinde
Gwamna ya shirya tattaunawa da kungiyoyin dake aikata ta'addanci a jiharsa Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Olatunbosun yace gwamnatin jiha tare da haɗin kan kungiyoyin yan Sa'kai ta shirya warware matsalolin dake tsakanin yan daban Anguya da yan Asiri.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A cewar kwamishinan wannan zubar da jinin da yaƙi ci yaƙi cinye wa lokaci ya yi da za'a kawo ƙarshen shi a jihar Oyo.

Meyasa gwamnati zata yi tattaunawar sulhu?

Da yake karin haske, Olatunbosun ya ce sun shirya taro ne domin warware matsalolin daga tushen su.

Ya bayyana cewa gwamnati zata yi aiki tare da hukumomin tsaro da Yan Sa'akai domin tattauna wa tsakanin ƙungiyoyin masu adawa da juna.

Ya ce:

"Majalisar zartarwan jiha na sane da ayyukan ta'addancin kungiyoyin asiri a faɗin Oyo, kuma zata zauna da su."
"Gwamnatin jihar Oyo, ƙarƙashin jagorancin gwamna Seyi Makinde, ta shirya kawo karshen faɗace-faɗace tsakanin waɗan nan ƙungiyoyin asirin."
"Zamu yi kokarin sasanta tsakanin su, su aje makaman su, su koma gida su rungumi zaman lafiya. Bayan haka zamu ɗaura ɗamarar yaƙi da duk kungiyoyin da suka ƙi ba mu haɗin kai."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Abba Kyari ya yi magana, ya bayyana kungiyoyi biyu dake kokarin ganin bayansa

A wani labarin na daban kuma Wani Mahaifi ya shararawa ɗiyar cikinsa mari, Allah ya mata rasuwa nan take a Jigawa

Yan sanda sun kama wani magidanci ɗan kimanin shekara 40 bisa zargin bugun ɗiyarsa Salima Hannafi, har lahira a jihar Jigawa.

Bayanai sun nuna cewa magidancin, Hannafi Yakubu, ya tafka wa yarinyar mari ne, kuma Allah ya karbi rayuwarta a karamar hukumar Babura.

Asali: Legit.ng

Online view pixel