Wani dan shekara 69 ya mutu a gidan magajiya a birnin tarayya Abuja

Wani dan shekara 69 ya mutu a gidan magajiya a birnin tarayya Abuja

  • Wani mutumi da ke gab da shiga shekaru 79 a duniya ya mutu a gidan magajiya a birnin tarayya Abuja ranar Litniin
  • Jami'an yan sanda sun dauke gawarsa kuma an damke yarinyar da ke tare da shi lokacin da ya mutu
  • Hukumar yan sanda bata saki jawabi kan lamarin ba har yanzu

Wani mutumi ya mutu a unguwar Kubwa dake karamar hukumar Bwari a birnin tarayya Abuja yayinda ya kai yarinya dalin Otal don shakatawa.

An tattaro cewa wannan abu ya faru ne da daren Litinin.

Mutumin mai suna, Ogunleye Emmanuel, ya shiga da yarinya dakin ne amma bai fito ba.

Wani mai gidan Otal a unguwar wanda ya bukaci a sakaye sunansa yace:

"Mutumin ya yanke jiki ya fadi yayinda yake tare da yarinyar."

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan ta'adda sun bindige tsohon dan takarar ciyaman da abokinsa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani dan shekara 69 ya mutu a gidan magajiya a birnin tarayya Abuja
Wani dan shekara 69 ya mutu a gidan magajiya a birnin tarayya Abuja
Asali: Instagram

Majiya ta bayyana cewa yan sandan Kubwa sun ziyarci wajen inda suka dauke gawar mutumin.

Wakilin DailyTrust yace sun fada masa cewa:

"Yan sanda na kokarin gano iyalinsa, an ajiye gawarsa a dakin ajiye gawawakin Kubwa General, Abuja."

Majiyar ta kara da cewa yan sanda sun tsare yarinyar.

Dillalin gidaje ya mutu a dakin Otal bayan shakatawa da matar aure

A wani labari mai kama da wannan, Wani dillalin gidaje, Diran Elijah, ya rasa rayuwarsa bayan jima'i da tsohuwar matarsa mai suna Idowu, a wani da dakin Otal dake unguwar Agbado a jihar Ogun.

Idowu da Elijah sun rabu shekaru hudu da suka gabata kuma dukkansu sun sake wani aure.

Idowu ta haifawa sabon mijinta yara biyu amma ta fita kwanciya da tsohon mijin.

Kara karanta wannan

Babu wani abu mai suna 'tubabben dan bindiga', kawai a kasheshu: El-Rufa'i

City Round ta ruwaito cewa sun hadu a Otal ne bayan Elijah ya kirata a waya domin sun hadu misalin karfe 10 na dare ranar Lahadi.

Bayan jami'in da suka yi, sai mutumin ya kwanta don hutawa kawai sai ya yanke jiki.

Kafin matar ta janyo hankali masu Otal din Elijah ya mutu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel