Bidiyo: Tsofaffin daliban UNIJOS sun nemo abokinsu da ya haukace, sun masa sha tara ta arziki

Bidiyo: Tsofaffin daliban UNIJOS sun nemo abokinsu da ya haukace, sun masa sha tara ta arziki

  • Allah ya sada wasu tsoffin daliban jami'ar Jos da wani abokin karatunsu da ya hadu da lalurar tabin hankali
  • Bayan haduwar ta su, cike da farin ciki suka rungumo abokin nasu mai suna Hilary Minabelem, ba tare da sun nuna kyamar tufafin da ke jikinsa ba
  • Haka kuma sun dauke shi zuwa asibitin masu tabin hankali inda suka biya domin a sanya shi a bangare na musamman sannan suka siya masa sabbin tufafi

Wasu tsoffin daliban jami’ar Jos (UNIJOS) sun yi wani abun a yaba masu inda suka sadu da wani abokin karatunsu da ya hadu da lalurar tabin hankali.

Tsoffin daliban dai sun bazama neman tsohon abokin karatun nasu mai suna Hilary Minabelem, wanda ya hadu da lalurar a ranar jajibirin kammala karatun digiri dinsa na biyu.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: An sake yi wa matafiya 'yan Kano da Nassarawa kisar gilla a hanyar Jos

Bidiyo: Tsofaffin daliban UNIJOS sun nemo abokinsu da ya haukace, sun masa sha tara ta arziki
Tsofaffin daliban UNIJOS sun nemo abokinsu da ya haukace, sun masa sha tara ta arziki Hoto: lindaikejiblogofficial
Asali: Instagram

Shafin Linda Ikeji ya rahoto cewa abokan karatun nasa sun baro gidajensu a Abuja sannan suka tsamo shi a titin Bakana da ke jihar Ribas.

A cikin bidiyon haduwar tasu, an gano Minabelem sanye da tufafi mai datti yayin da abokan karatun nasa suka kewaye shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Har ila yau an jiyo wata daga cikinsu tana ce masa kalli Sulaiman dinka inda suka fashe da dariya yayin da suka rungume juna da shi da wanda aka kira da Sulaiman din.

A ruwayar Punch, mun ji cewa abokan nasa sun dauke shi zuwa asibitin masu laluran tabin hankali da ke Rumuigbo, Port Harcourt domin samun kulawar likitoci.

Sun kuma hada kudi kimanin N320,000 saboda a sanya shi a bangare mai zaman kansa a zaman da zai yi na samun kulawar likitoci, sannan kuma sun siya masa sabbin tufafi.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali yayin da tsohon Sarki Sanusi II ya shirya kai ziyara jihar Kano

Kalli bidiyon haduwar tasu a kasa:

Kotu ta sa a yi wa matashin ɗan kasuwa Bulala Bakwai a jihar Kaduna

A wani labari na daban, wata Kotun Majistire a Kaduna ta yanke wa wani matashi ɗan shekara 25, Nasiru Ahmed, hukuncin bulala bakwai kan satar buhunan Gishiri guda biyar.

Matashin mai sana'ar Tireda ta saye da siyarwa na zaune ne a Anguwar Tudun Wada, dake cikin birnin Kaduna, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

An gurfanar da Ahmad ne a gaban Kotu, bisa tuhumar fasa shago da kuma aikata sata a shagon.

Asali: Legit.ng

Online view pixel