Da dumi-dumi: Shugaba Buhari zai shilla kasar Belgium halartar wani taro

Da dumi-dumi: Shugaba Buhari zai shilla kasar Belgium halartar wani taro

  • Fadar shugaban kasa ta fitar da sanarwar cewa, shugaban kasa zai yi tafiya daga Najeriya zuwa kasar Belgium
  • Tafiyar shugaban za ta fara ne daga yau, inda zai shafe kwanaki kafin ya dawo a karshen makon nan
  • Sanarwar ta ce, shugaban zai halarci wani taron shugabannin duniya ne da za a yi a kasar Belgium

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar Najeriya a yau dinnan zuwa kasar Belgium domin halartar wani taron shugabannin duniya.

Sanarwar da Legit.ng Hausa ta samo daga mai taimakawa Buhari a harkokin yada labarai ta ce, shugaban zai dawo Najeriya ranar Asabar idan Allah ya kaimu.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tafi Beligum
Da dumi-dumi: Shugaba Buhari zai cilla kasar Belgium halartar wani taro | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Sanarwar ta karanta cewa:

"A yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar Abuja domin halartar taron shugabannin kasashen Turai da na Afirka da kuma shugabannin kungiyoyi da dama a taron kungiyar Tarayyar Turai da kasashen Afirka (EU-AU) karo na 6 a birnin Brussels na kasar Belgium. Ana sa ran shugaban zai dawo kasar ranar Asabar."

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: ASUU zata shiga yajin aiki, amma na jan kunne na wata guda

'Yan Najeriya da dama na nuna damuwa kan yadda Shugaba Buhari ke ci gaba da fita kasashen waje da sunan halartar taruka.

Dirarsa ke da wuya, Shugaba Buhari ya gana da Shugaban kasar Turkiyya

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da Shugaban kasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, da safiyar Juma’a, 17 ga Disamba, 2021 a birnin Istanbul.

Hadimin Shugaban Kasan, Buhari Sallau, ya bayyana hakan a hotunan da ya saki a shafinsa na Facebook.

Shugabannin kasashen biyu sun yi zaman diflomasiyya tare Istanbul. Wannan ganawa ya faru ne bayan da ya dira tashar jirgin birnin Istanbul.

Asali: Legit.ng

Online view pixel