Babu kotun da ta isa ta hanamu tsige Mahdi Aliyu Gusau, majalisar dokokin Zamfara

Babu kotun da ta isa ta hanamu tsige Mahdi Aliyu Gusau, majalisar dokokin Zamfara

  • Majalisar dokokin jihar Zamfara ta yi martani da shigar da ita kotu da mataimakin gwamnan jihar yayi
  • Kakakin majalisar ya bayyana cewa abinda suke daidai ne saboda haka babu kotun da zata iya hansu
  • A cewarsa, laifuka hudu ake tuhumar mataimakin gwamnan dasu kuma za'a yi bincike kan hakan

Zamfara - Majalisar dokokin jihar Zamfara a ranar Talata ta bayyana cewa babu kotun da ta isa ta hanasu tsige mataimakin gwamnan jihar, Barista Mahdi Aliyu Gusau.

Shugaban kwamitin yada labaran majalisar, Alhaji Shamsudden Bosko, ya bayyana hakan ne yayin hira da manema labarai a Gusau, birnin jihar., rahoton DailyTrust.

Bosko yace shirin tsige mataimakin gwamnan ya bi tsarin sashe na 188(5)(7) na kundin tsarin mulkin Najeriya saboda haka, "babu kotun da zata iya hana tsigeshi"

A cewarsa, yan majalisa 18 cikin 24 ne suka amince kan tuhumu-tuhumen da ake yiwa mataimakin gwamnan.

Kara karanta wannan

Zamfara: Majalisa ta sake aike wa da zazzafan sako ga mataimakin Matawalle kan batun tsige shi

Mahdi Aliyu Gusau, majalisar dokokin Zamfara
Babu kotun da ta isa ta hanamu tsige Mahdi Aliyu Gusau, majalisar dokokin Zamfara Hoto: Mahdi Gusau
Asali: UGC

Kotu ta dage zaman bukatar mataimakin gwamna Matawalle da jam'iyyar PDP

Babbar Kotun tarayya dake zamanta a Abuja, ta yi fatali da bukatar mataimakin gwamnan Zamfara Mahdi Aliyu Gusau, da jam'iyyarsa ta PDP ranar Talata, 15 ga Febrairu, 2022.

Maimakon haka alƙalin ya saka ranar 10 ga watan Maris, 2022 a matsayin ranar da za'a dawo don cigaba da fafata shari'ar.

Shugabar Alkalan jihar Zamfara ta kafa kwamitin bincike kan Mahdi Gusau

Shugaban Alkalan jihar Zamfara, Mai Shari'a Kulu Aliyu, ta kafa kwamitin mutum bakwai don gudanar da bincike kan tuhume-tuhumen da majalisar dokokin jihar ke wa mataimakin gwamnan Zamfara, Mahdi Gusau.

Mai Shari'a Kulu Aliyu ta rantsar da kwamitin ne ranar Litinin kuma ta nada tsohon Alkali, Tanko Soba, matsayin shugaban kwamitin

Kara karanta wannan

Zamfara: Kotu ta yi watsi da bukatar mataimakin gwamna Matawalle da jam'iyyar PDP

Ayyukan kwamitin a cewarta sun hada da bincike kan tuhumar almundahana, ci da ofis, saba kundin tsarin mulki da kuma yin abubuwan da basu dace ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel