Zamfara: Ba Umarnin Kotun da zai hana mu tsige mataimakin gwamna, Majalisa

Zamfara: Ba Umarnin Kotun da zai hana mu tsige mataimakin gwamna, Majalisa

  • Majalisar dokokin Zamfara ta ce babu wani umarnin kotu da zai dakatar da ita daga tsige mataimakin gwamna, Mahdi Aliyu
  • A ranar Litinin, kotun tarayya dake zama a Abuja ta saka ranar zaman karar da Mahdi ya shigar ta neman dakatar da majalisa
  • Shugaban kwamitin bayanai, Alhaji Bosko, ya ce kudirin ya dace da kwansutushin ɗin Najeriya

Zamfara - Majalisar dokokin jihar Zamfara, a ranar Talata, ta ce babu wani umarnin kotu da zai dakatar da ita daga tsige mataimakin gwamna, Mahdi Aliyu Gusau.

Daily Trust ta rahoto cewa shugaban kwamitin bayanai, Alhaji Shamsuddeen Bosko, shi ne ya faɗi matsayar majalisar a wani taron manema labarai a Gusau.

Bosko ya yi bayanin cewa shirin tsige mataimakin gwamnan ya yi dai-dai da dokar sashi na 188 (5) (7) a kundun dokokin mulkin tarayyan Najeriya.

Kara karanta wannan

Babu kotun da ta isa ta hanamu tsige Mahdi Aliyu Gusau, majalisar dokokin Zamfara

Bisa haka, a cewarsa, "Babu wani umarnin Kotu da zai dakatar da majalisar dokokin Zamfara daga tsige mataimakin gwamnan."

Majalisar dokokin Zamfara
Zamfara: Ba Umarnin Kotun da zai hana mu tsige mataimakin gwamna, Majalisa Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Honorabul Bosko ya ƙara da cewa a halin yanzun yan majalisu 18 daga cikin 24 sun kaɗa kuri'ar amincewa da shirin a zaman majalisar, kamar yadda Tribune ta rahoto.

Ya ce mambobin majalisa sun amince ne bayan an gabatar da zarge-zagen da ake masa da suka haɗa da, badakalar kuɗaɗe, rashin ɗa'a, da kuma ƙin biyayya ga umarnin ayyukan da aka ɗora masa.

Wane hali ake ciki a Kotu?

Babbar kotun tarayya dake Abuja ta zaɓi ranar 10 ga watan Maris, 2022 domin zaman sauraron ƙarar mataimakin gwamnan, inda ya bukaci Kotu ta dakatar da shirin majalisa a kansa.

Mai Shari'a Inyang Ekwo, a ranar Litinin, ya ɗage zaman, kuma ya umarci kowane ɓangaren ya kawo masa Fayil da abubuwan da suka shafi ƙarar kafin zaman gaba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari ya soke taronsa da gwamnonin APC bayan sun hallara, zai shilla turai

Idan baku manta ba a wannan rana ta Litinin, Babbar Alkalin jihar, Kulu Aliyu, ta kaddamar da kwamitin mutum 7 da za su bincike zargin da ake wa Mahdi Aliyu.

A wani labarin kuma Atiku ya gana da gwamnoni, jagororin jam'iyyar APC, ya faɗi gaskiyar abin da ya faru

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya musanta ganawar sirri da gwamnonin jam'iyyar APC, da jagororinta.

Atiku, wanda ya yi karin haske ta bakin kakakinsa, Paul Ibe, yace ya je ta'aziyyar mahaifiyar Mangal a Katsina, kuma ya haɗu da jagororin APC a can.

Asali: Legit.ng

Online view pixel