Bidiyon Sanata yana girgijewa a cikin dakinsa, ya na nuna bajintarsa a fannin rawa

Bidiyon Sanata yana girgijewa a cikin dakinsa, ya na nuna bajintarsa a fannin rawa

  • A wani bidiyo dake yawo a kafafen sada zumuntar zamani anga Sanata Jarigbe Agom, wanda a yanzu yake wakiltar arewancin Cross River a majalisar dattawa yana bin waka gami da kwasar rawa
  • Dan siyasan yana rawan wata waka da mawaki Fireboy DML yayi wacce ya sanya wa suna 'Scatter' rawa da tsarin rawan da yayi matukar kayatar da abokan sa na Facebook.
  • Hakan yasa abokan sa da mabiyan sa na Facebook suke ta kara wallafa bidiyon, wanda ke bayyana yadda Sanatan na su yayi matukar iya rawa

Wani Sanatan Najeriya, Jarigbe Agom, wanda ke wakiltar Arewacin Cross River a majalisar dattawa, an gan shi yana rawan wata waka Scatter da mawaki Fireboy DML ya rera.

Bidiyon salon rawan nashi mai birgewa ya kayatar da abokan shi da sauran mabiyan shi, hakan yasa suka yi hanzarin cigaba da wallafawa a Facebook.

Kara karanta wannan

Matashi mai shekaru 19 ya dirka wa malamar shi mai shekaru 28 ciki, za ta haife shi

Bidiyon Sanata yana girgijewa a cikin dakinsa, ya na nuna bajintarsa a fannin rawa
Bidiyon Sanata yana girgijewa a cikin dakinsa, ya na nuna bajintarsa a fannin rawa. Hoto daga Tom Alims
Asali: Facebook

Ya kwashi rawan ne don nuna farinciki a kan nasarar zabe. Duk da ba a san takamaiman dalilin da yasa yake rawa cikin tsananin farinciki ba, ana iya jin hayaniyar PDP a cikin bidiyon, hakan na nuna watakila yana murnar nasarar da jam'iyyar shi tayi ranar Asabar a zaben karamar hukuma a Abuja.

Yayin da Tom Alims ya wallafa bidiyon a Facebook, ya rubuta: "Sanatan mu mai murnar nasara. Yana ta rawa tun shekarar da ta gabata."

Me jama'a ke cewa a kan bidiyon?

Mutane sun yi tsokaci iri-iri game da yadda Sanata Jarigbe Agom yake kwasar rawa. Yayin da aka wallafa bidiyon a Facebook, nan da nan mabiyan shi da masoya suka fara tsokaci suna cigaba da wallafa bidiyon suna tsokaci. Da yawan su sun yaba mishi na zama Sanata mai salo.

Kara karanta wannan

Duniya kenan: Mai shekaru 16 ya saci yarinya 'yar shekaru 4, ya nemi fansan N70,000 a Katsina

Ga wasu daga cikin tsokacin da mutane suka yi:

Tsokacin Joe Ulom : "Sanata mai salon zamani."
Shi kam Odo Joseph cewa yayi: "Za ku iya kara cewa, mai girma Sanatan mu Jarigbe Agom na jin dadin sa."
Inda Derek Omini ya ce: "Ka cigaba da jin dadin ka kaji."

Bidiyon biloniya Dangote ya na kwasar rawa a wurin wani biki ya kayatar

A wani labari na daban, nishadi ba ya kebantuwa ga talaka ko mai arziki, komai arzikin mutum, ya na bukatar nishadi a wasu lokutan.

Idan aka yi maganar hamshakin mai arziki kamar Alhaji Aliko Dangote, wasu za su ce ba shi da lokacin halartar bukukuwa.

Sai dai ba hakan ba ne ga hamshakin mai arzikin Afrikan kuma bakar fatan da ya fi kowa arziki a duniya, ya na shiga nishadi a lokuta da dama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel