Bidiyon biloniya Dangote ya na kwasar rawa a wurin wani biki ya kayatar

Bidiyon biloniya Dangote ya na kwasar rawa a wurin wani biki ya kayatar

  • Bidiyon biloniyan mai arzikin Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya na warwasawa tare da kwasar rawa cike da nishadi a wurin wani biki ya kayatar
  • Kamar yadda shafin @arewafamilyweddings suka wallafa a Instagram, an ga Aliko Dangote ya na rawa a wurin da ya fi kama da biki
  • Ya na sanye da kaftani mai launin baki yayin da sauran wadanda ke wurin suke sanye da manyan kaya, lamarin da ke bayyana liyafar biki ce

Nishadi ba ya kebantuwa ga talaka ko mai arziki, komai arzikin mutum, ya na bukatar nishadi a wasu lokutan.

Idan aka yi maganar hamshakin mai arziki kamar Alhaji Aliko Dangote, wasu za su ce ba shi da lokacin halartar bukukuwa.

Bidiyon biloniya Dangote ya na kwasar rawa a wurin wani biki ya kayatar
Bidiyon biloniya Dangote ya na kwasar rawa a wurin wani biki ya kayatar. Hoto daga @arewafamilyweddings
Asali: Instagram

Sai dai ba hakan ba ne ga hamshakin mai arzikin Afrikan kuma bakar fatan da ya fi kowa arziki a duniya, ya na shiga nishadi a lokuta da dama.

Kara karanta wannan

Sabbin bayanai 4 game da Dangote da baku sani ba: Zai iya kashe N415m kullum na tsawon shekaru 40

Bidiyon biloniya kuma hamshakin mai arzikin Afrika, Alhaji Aliko Dangote, ya na kwasar rawa cike da birgewa a wurin wani biki ya matukar kayatarwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda bidiyon da @arewafamilyweddings suka wallafa a shafin su na Instagram ya bayyana, an ga hamshakin mai arzikin sanye da manyan kaya, lamarin da ke tabbatar da cewa wurin biki ne.

Martanin jama'a

Ganin bidiyon nan ke da wuya jama'a suka fara martani a kai

@zarah_queenn cewa ta yi:

"Kuma ya iya rawa fa na wa oooooooooo"

@zee_shoeskd ta yi martani da:

"Ka ga rawan masu kudi! Ba hayaniya."

@drockdcollins martani ya yi da cewa:

"gayen ya iya rawa kuwa".

@mahmuska ta ce:

"Ya ko iya rawa."

Bidiyo: Diyar biloniya Dangote, Halima Dangote ta gigita masu kallo da salon rawanta

A wani labari na daban, Diyar attajirin dan kasuwar nan, Aliko Dangote, Halima, ta zamanto abar labari a kafafen sada zumuntar zamani domin ta burge jama'a kwarai.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Malaman makarantun firamare a Abuja sun tsunduma yajin aiki

Matar mai karancin shekaru wacce kowa ya sani da matukar tsantseni da kamun kai ta bayyana tana kwasar rawa mai daukar hankali a wani taro da ta je.

Ba kamar yadda ake zato ba, cikin kwarewa Halima ta bayyana a fili tana rawa tare da bin wakar wani mawaki sanannen mai suna Teni, cike da shauki.

Ko kadan ba a hango tsoro ko shakka tattare da Halima ba domin cikin kwarewa ta kwashi rawar. Take a nan masoya cike da shauki da begenta suka yi ta yada bidiyon Halima Dangote tana rawar wacce ta tafi da tunaninsu har da damansu suke tsokaci iri-iri akai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel