Abba Kyari: Sunayen manyan 'yan sanda 5 da aka kwamushe tare da mikawa NDLEA

Abba Kyari: Sunayen manyan 'yan sanda 5 da aka kwamushe tare da mikawa NDLEA

  • Bayan NDLEA ta fitar da sanarwar cewa ta na neman Abba Kyari ido rufe, hukumar 'yan sanda ta cafke shi da wasu manyan jami'ai hudu
  • Wurin karfe 5 na yammacin Litinin 'yan sandan Najeriya suka mika DCP Abba Kyari, ACP Sunday J. Ubua, ASP Bawa James, Sifeta Simon Agirgba, Sifeta John Nuhu
  • Sai dai hukumar 'yan sandan ta ce akwai AS John Umoru wanda ba a kama shi ba har yanzu, za ta cigaba da tabbatar da bin dokar kasar nan

FCT, Abuja - A ranar Litinin, 14 ga watan Fabrairu, 'yan sanda sun yi ram da DCP Abba Kyari da wasu jami'an 'yan sanda hudu kan zargin alaka da safarar miyagun kwayoyi tsakanin kasashe.

Kyari wanda a halin yanzu an dakatar da shi, ana zarginsa da hannu a hada kai wurin aikata laifi, rashawa, kwashe shaidu a wata harkallar ta safarar miyagun kwayoyi tsakanin kasashen duniya.

Kara karanta wannan

Jerin Manyan abubuwa 5 da suka faru da jarumin dan sanda Abba Kyari tun farkon tuhumarsa

Abba Kyari: Sunayen manyan 'yan sanda 5 da aka kwamushe tare da mikawa NDLEA
Abba Kyari: Sunayen manyan 'yan sanda 5 da aka kwamushe tare da mikawa NDLEA. Hoto daga vanguardngr.com
Asali: UGC

An yi wannan kamne ne bayan hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyin ta bayyana cewa tana neman Kyari da wasu mutum hudu ido rufe.

Ga jerin sunayen manyan 'yan sandan da aka damke:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

  1. DCP Abba Kyari
  2. ACP Sunday J. Ubua
  3. ASP Bawa James
  4. Inspector Simon Agirgba
  5. Inspector John Nuhu

A wata takarda da 'yan sanda suka fitar, an gano cewa har yanzu ba a kama AS John Umoru ba.

NDLEA ta tabbatar da cewa biyar daga cikin jami'an 'yan sandan an kai su hedkwatar su ne wurin karfe 5 na yammacin ranar Litinin kuma an mika su hannun hukumar domin tuhuma da cigaban bincike.

Bayan mika jami'an 'yan sandan hannun NDLEA, sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya yi kira ga shugaban hukumar NDLEA, Buba Marwa da ya tabbatar an "tsamo, kama da kuma bincikar jami'an hukumarsa da ke da hannu a safarar miyagun kwayoyin".

Kara karanta wannan

Sunayen abokan harkallar Kyari 2 da jami'an NDLEA dake da hannu a safarar miyagun kwayoyi

Sifeta janar din 'yan sandan Najeriya ya tabbatarwa da 'yan Najeriya cewa mulkinsa zai cigaba da tabbatar da an bi dokokin aikin 'yan sanda, dawo da martabarsu, assasa yaki da rashawa, mutunta dokar kasa da kuma ta sauran hukumomi.

Sunayen abokan harkallar Kyari 2 da jami'an NDLEA dake da hannu a safarar miyagun kwayoyi

A wani labari na daban, a ranar Litinin, hedkwatar 'yan sandan Najeriya ta bayyana sunayen wadanda ake zargi da hada kai da DSP Abba Kyari da wasu 'yan sanda hudu wurin shigo da miyagun kwayoyi cikin kasar nan.

Hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi, NDLEA a ranar Litinin ta bayyana ta na neman Abba Kyari da tawagarsa, rahoton Premium Times ya bayyana.

'Yan sanda daga bisani sun damke wadanda ake zargi tare da mika su hannun hukumar yaki da fasa kwabrin miyagun kwayoyin domin cigaba da bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel