Yanzu-yanzu: ASUU zata shiga yajin aiki, amma na jan kunne na wata guda

Yanzu-yanzu: ASUU zata shiga yajin aiki, amma na jan kunne na wata guda

Bayan dogon zaman da kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ASUU tayi cikin daren Litinin, majalisar zartaswar kungiyar ta amince za a tafi yajin aikin jan kunnen gwamnatin tarayya a amsa bukacinsu.

Vanguard ta ruwaito wata majiya daga cikin ganawar cewa ASUU ta yanke wannan shawara ne don baiwa Gwamnatin Tarayya damar yin abinda ya kamata ko kuma su tafi yajin aikin din-din-din.

ASUU NEC
Yanzu-yanzu: ASUU ta shiga yajin aiki, amma na jan kunne na wata guda
Asali: Facebook

A cewar majiyar:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Kawai muna son baiwa gwamnati dama ne don tayi abinda ya dace domin hana yajin aikin din-din-din. Mu ma fa iyaye ne kuma 'yayanmu na karatu a jami'o'in amma ba zamu zuba ido harkar ilimi ta lalace a kasar nan ba."

Kara karanta wannan

Sojojin sun hallaka yan bindiga 20 da suka yi kokarin sake kai hari makarantar Soji NDA

"Muna wannan gwagwarmaya ne domin amfanin kowa, dukkanmu zamu ji dadi idan aka gyara. Manyan masu fada aji sun sanya baki amma da alamun gwamnati bata shirya ba. Shugabanmu zai yi bayani ga yan jarida an jima."

Asali: Legit.ng

Online view pixel