Pantami ya kaddamar da muhimmin aiki a mahaifar Shugaba Buhari

Pantami ya kaddamar da muhimmin aiki a mahaifar Shugaba Buhari

  • Minista Ali Pantami ya kaddamar da cibiyar fasahar sadarwa ta Muhammadu Buhari a jihar Katsina
  • Pantami ya kaddamar da cibiyar wacce hukumar kula da ci gaban fasahar Sadarwa ta Najeriya (NITDA) ta gina a ranar Talata, 15 ga watan Fabrairu
  • Hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar

Katsina - Ministan harkokin sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami, ya kaddamar da cibiyar fasahar sadarwa ta Muhammadu Buhari.

Pantami ya kaddamar da cibiyar ne a ranar Talata, 15 ga watan Fabrairu, a mahaifar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta jihar Katsina.

Pantami ya kaddamar da muhimmin aiki a mahaifar Shugaba Buhari
Pantami ya kaddamar da muhimmin aiki a mahaifar Shugaba Buhari Hoto: prnigeria.com
Asali: UGC

A wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara a kafofin sadarwar zamani, Bashir Ahmad ya fitar a shafinsa na Twitter, ya bayyana cewa hukumar kula da ci gaban fasahar Sadarwa ta Najeriya (NITDA) ce ta gina cibiyar.

Kara karanta wannan

Ku taimaka ku sake damƙa amanar Najeriya hannun APC a 2023, Lawan ya roki yan Najeriya

Bashir ya rubuta a shafin nasa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ministan harkokin sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya kaddamar da cibiyar fasahar sadarwa ta Muhammadu Buhari wanda hukumar @NITDANigeria ta gina, a yau a jihar Katsina. #DigitalNigeria”

Martanin jama'a

Mabiya shafin Bashir da dama sun yi martani, inda suka kalubalance shi kan dalilin da yasa ya kira ministan da farfesa bayan kungiyar malaman ASUU ta ce bai cancanta ba.

Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:

@Societal_Doctor ya yi martani:

“Kungiyar ASUU ta ce shi ba farfesa bane, kuma kana kiransa da hakan, zaka iya fada mani dalili?”

Drmuzoic ta ce:

“Baka ji hukuncin malaman ASUU kan farfesancin ba?"

@ytkameenu ya ce:

“. Da fatan ka toshe ASUU, kwanan nan za a soke satifiket dinka kaima.”

@Paulj4u ya ce:

Kara karanta wannan

Rikicin APC a Kano: Dattawan jihar sun shiga tsakanin tsagin Ganduje da Shekarau

“Har yanzu ko kunya baka ji kana kiransa farfesa. Allah ya kyauta”

ASUU tace Pantami bai cancanci zama Farfesa ba, zata hukunta FUTO

A gefe guda, mun kawo a baya cewa kungiyar malaman jami'o'i ASUU ta yi watsi da matsayin Farfesa da aka bai wa ministan harkokin sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Dakta Isa Pantami.

Punch ta rahoto cewa ƙungiyar bayan taron mambobin majalisar zartarwan ta da ya gudana yau, ta bayyana baiwa Pantami Farfesa a matsayin, "karan tsaye ga doka."

Shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa, Emmanuel Osodeke, shi ne ya bayyana haka a wurin taron manema labarai da ƙungiyar ta kira ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel