Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga sun bindige yan sanda uku har lahira a Ofis

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga sun bindige yan sanda uku har lahira a Ofis

  • Yan bindiga sun sake halaka jami'an yan sanda guda uku a wani hari da suka kai kusa da caji Ofis a Ebonyi
  • Wata majiya ta bayyana cewa yan sandan sun rasa rayukan su ne yayin da yan bindigan suka buɗe musu wuta a kan hanyar Abakalike zuwa Enugu
  • Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar, Loveth Odah, ta tabbatar da lamarin amma tace zata kai ziyara wurin tukunna

Ebonyi - Wasu miyagun yan bindiga sun halaka jami'an yan sanda uku a jihar Ebonyi, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Wata majiya mai ƙarfi ta shaida mana cewa yan ta'addan sun bindige yan sandan har Lahira ne da daren ranar Litinin a gaban Caji Ofis dake kan babbar hanyar Enugu-Abakaliki.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum Alheri ne ga al'ummar duniya gaba daya, Sanata Kashim Shettima

Yan bindiga
Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga sun bindige yan sanda uku har lahira a Ofis Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Yan sandan, waɗan da aka rahoto sun saka shinge a kan hanya, sun rasa rayuwarsu ne yayin da yan bindigan suka farmake su, kuma suka buɗe musu wuta.

Majiyar ta ƙara da cewa yan bindiga sun zo ne a cikin babbar Motar Bas, wanda yan sandan suka yi tsammanin motar yan kasuwa ce.

Premium times ta rahoto Majiyar ta ce:

"An kai gawarwakin yan sandan uku zuwa ɗakin ajiye gawa dake Abakalike bayan likitoci sun tabbatar da cewa sun mutu."

An kashe yan sanda a Enugu

Aƙalla yan sanda 10 ne suka rasa rayukan su a hare-haren yan bindiga kala daban- daban a jihar Enugu makon da ya gabata.

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindiga sun matsa wa yan sanda ta hanyar kai musu hari a shingen binciken ababaen hawa a yankunan jihar.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: ASUU zata shiga yajin aiki, amma na jan kunne na wata guda

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar, Loveth Odah, ta tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai.

Sai dai ta ce ba zata iya bada cikakken bayani kan adadin waɗan da suka rasa, rayukan su ba har sai ta ziyarci wurin da lamarin ya faru.

A wani labarin na daban kuma mun tattaro muku Manyan taƙaddama 5 da suka baibaye jarumin dan sanda Abba Kyari tun farko

Mataimakin kwamishinan yan sanda, DCP Abba Kyari, ya fara shiga zargi ne tun shekarar da ta gabata.

Fitaccen ɗan damfaran nan na Intanet, Hushpuppi, shi ne ya fara saka gwarzon ɗan sandan cikin lamarin damfara a Amurka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel