Yajin-aiki: Kungiyar Dalibai ta fadi matakin da za ta dauka kan ASUU da Gwamnatin Buhari

Yajin-aiki: Kungiyar Dalibai ta fadi matakin da za ta dauka kan ASUU da Gwamnatin Buhari

  • Kungiyar daliban Najeriya ta NANS ta yi magana a game da sabon yajin-aikin da ASUU ta shiga
  • Shugaban NANS, Asefon Sunday ya fitar da jawabi inda ya yi wa gwamnati da ASUU kaca-kaca
  • Asefon Sunday ya daura laifi a kan gwamnati da malaman jami’a, ya ce dalibai za su yi zanga-zanga

Abuja - Jaridar Punch ta rahoto cewa kungiyar daliban Najeriya watau NANS, ta yi Allah-wadai da sabon yajin-aikin da malaman jami’a su ka sake tafiya.

A ranar Litinin, 14 ga watan Fubrairu 2022 ne shugaban kungiyar NANS na kasa, Asefon Sunday ya fitar da jawabi, yana kokawa a kan wannan yajin-aikin.

Sunday ya yi wa jawabin da ya fitar take da ‘ASUU Warning Strike: A Reckless Irresponsibility’.

Asefon Sunday ya hada da gwamnatin tarayya da shugabannin ASUU, ya yi masu ta-tas a kan yadda suka gaza shawo kan batun ba tare da rufe jami’o’i ba.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: NDLEA ta cafke Mutumin Indiya da aka samu da kwalaben codeine 134,000

“Mun samu labarin matakin da kungiyar ASUU ta dauka na shiga yajin-aikin jan-kunne na tsawon wata daya tattare da matukar takaici.”
“Mun yi tunanin ASUU da FG za su nemi hanyar da za su cinma maslaha, a dauki matakin da ya dace na bunkasa harkar ilmi.” - Asefon Sunday

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kungiyar Dalibai
'Yan Kungiyar NANS su na zanga-zanga Hoto: www.sunnewsonline.com
Asali: UGC

Asefon Sunday: Za ayi zanga-zanga

Kamar yadda The Eagle ta kawo rahoto, Sunday ya ce kungiyar daliban za ta shirya zanga-zanga a fadin kasar nan domin su nunawa kowa rashin jin dadinsu.

Kungiyar ta ce ba za ta sauka daga matsayar zanga-zanga ba har sai an janye yajin-aikin. Sunday ya yi kira ga Chris Ngige da wakilan ASUU su koma kan tebur.

Laifun dukkansu ne - NANS

Shugaban daliban ya zargi kowane bangare da saba doka da rashin yin abin da ya kamata, wanda hakan ya jawo sabanin ya kai ga an tafi yajin-aikin makonni hudu.

Kara karanta wannan

Karya ta kare: Abin da mutane ke cewa da NDLEA ta zargi Abba Kyari da safarar kwayoyi

A cewar Sunday, gwamnatin Najeriya da malaman jami’ar sun sa son-kai a wajen tattaunawar, ba su yi la’akari da halin da dalibai suke ciki ko wanda za su shiga ba.

NANS ta ce gwamnati ba tayi kokarin hana ASUU zuwa yajin-aiki ba. Sannan ta nemi a rika hadawa da wakilan dalibai idan malamai za su gana da gwamnati.

ASUU ta rufe jami'o'i

Hakan ya biyo bayan sanarwar da shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke ya bada a jiya.

Idan za a tuna, kungiyar malaman jami'a ta ASUU ta ayyana shigarta cikakken yajin aiki bayan tattaunawa mai zurfi da majalisar zartarwarta ta yi a garin Legas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel