Asiri ya tonu: NDLEA ta cafke Mutumin Indiya da aka samu da kwalaben codeine 134, 000

Asiri ya tonu: NDLEA ta cafke Mutumin Indiya da aka samu da kwalaben codeine 134, 000

  • Hukumar NDLEA ta kasa ta ce wani mutumin kasar Indiya da ya shigo da kwayoyi ya fado hannunta
  • Jami’an DSS ne suka taimaka wajen cafke Vyapak Nutal bayan ya tare a wani otel a garin Sokoto
  • Nutal ya labe yana neman wanda zai saye tulin kwalaben Codeine da ya shigo da su ta iyakar Illela

Abuja - Hukumar NDLEA da ke yaki da masu safarar miyagun kwayoyi a Najeriya ta kama wani Ba’Indiye Vyapak Nutal da zargin shigo da kwayoyi.

Hukumar ta na tuhumar Vyapak Nutal da laifin shigo da kwalabe 134,700 na codeine. Gidan talabijin nan na Channels TV ta fitar da wannan rahoto.

Mai magana da yawun bakin NDLEA na kasa, Femi Babafemi ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar a ranar Lahadi, 13 ga watan Fubrairu 2020.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An mika Abba Kyari ga NDLEA bayan kamo shi da abokan harkallarsa

Femi Babafemi ya ce an shigo da kwalaben na codeine ta iyakar Najeriya da Nijar a jihar Sokoto.

“Wanda ake zargi ya lodo kwayoyin a cikin motoci a Cotonou, kasar Benin, ya shigo da su ta iyakar Najeriya da Jamhuriyar Nijar a Illela, Sokoto.”
NDLEA sun kama shi
Vyapak Nutal Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC
“(Vyapak Nutal) ya tare a wani otel a jihar Sokoto. Bayanai sun nuna mana cewa Nutal ya fara neman masu sayen miyagun kwayoyin da ya kawo.”
“Ana cikin bin sahunsa ne sai dakarun DSS suka yi nasarar cafke shi, suka mika shi ga jami’an NDLEA a ranar Laraba, 10 ga watan Fubrairu, 2022.”

- Femi Babafemi

Kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta bayyana, Nutal mutumin kasar Indiya ne da ya shigo Najeriya.

A daidai wannan lokaci kuma aka ji cewa hukumar ta kama wasu mutane da suka yi yunkurin shigo da miyagun kwayoyi ta filin jirgin sama na MMIA.

Kara karanta wannan

Ku taimaka ku sake damƙa amanar Najeriya hannun APC a 2023, Lawan ya roki yan Najeriya

Jaridar ta ce kwayoyin da aka yi kokarin safararsu zuwa Najeriya sun hada da hodar iblis, Methamphetamine, Khat, Tramadol da kuma tabar wiwi.

Badakalar Abba Kyari

Ku na da labari cewa a ranar Litinin, 14 ga watan Fubrairu 2022 ne NDLEA ta bada sanarwar ta na neman DCP Abba Kyari da hannu wajen safarar kwayoyi.

Hukumar ta ce ta na zargin jami’in ‘Dan Sandan da aka dakatar da hannu wajen safarar kwayoyi. Rahotanni su na zuwa mana cewa Kyari ya shiga hannu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel