Karya ta kare: Abin da mutane ke cewa da NDLEA ta zargi Abba Kyari da safarar kwayoyi

Karya ta kare: Abin da mutane ke cewa da NDLEA ta zargi Abba Kyari da safarar kwayoyi

  • A ranar Litinin, 14 ga watan Fubrairu 2022 ne NDLEA ta bada sanarwar ta na neman DCP Abba Kyari
  • Hukumar ta ce ta na zargin jami’in ‘Dan Sandan da aka dakatar da hannu wajen safarar kwayoyi
  • Mutane su na tofa albarkacin bakinsu, har ta kai ana cewa a binciki wadanda Kyari ya kama a baya

Legit.ng Hausa ta tattaro wasu daga cikin abubuwan da mutane suke fada a shafin Twitter:

NDLEA ta na neman Abba Kyari. Ta na zarginsa da hannu a safarar kwayoyi tsakanin kasa-da-kasa. Kwanakin baya FBI ta ce yana cikin mutanen Hushpuppi. Karyarsa ta kare kenan?

- Ogbeni Dipo

Abba Kyari ya na cikin babbar matsala.

- Ameenu Kutama

Ta Abba Kyari ta kare. Ina mamaki an yi lokacin da aka yi masa lakabi da gwarzon ‘Dan Sanda.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: An mika Abba Kyari ga NDLEA bayan kamo shi da abokan harkallarsa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

- Man Of Letters

Abba Kyari yana can yana yi mana dariya a yanzu. Tun Yuli FBI ta ke nemansa, aka dakatar da shi daga aiki a Agusta. Tun a watan gwamnatin Najeriya ta ke bincikensa. Har zuwa Fubrairu, yana yawo hankalinsa kwance. Ana zarginsa da hada-kai da gawurtattun marasa gaskiya.

- Fisayo Sayombo

Abba Kyari dai ya iya abubuwa dabam-dabam. Da safe ya yi aikin ‘Dan Sanda. Da maraice ya zama tela. Cikin dare kuma ya zama malamin kwaya.

- Sadiq Tade

Wani Ayobami ya ce:

“A lokacin da aka dakatar da dakarun Abba Kyari, sun kama wani mai safarar kwayoyi a Enugu da kilo 25 na hodar iblis. Sai ya kira NDLEA domin ta saki kilo 10 na kwayar, ya canza sauran da kwayar karya, ya saida duk kilon wancan a kan N7m a kasuwa.”

Kara karanta wannan

Jerin gaskiya 12 da baku sani ba game da ɗan sanda Abba Kyari da aka damke

Karya ta kare: Abin da mutane ke cewa da NDLEA ta zargi Abba Kyari da safarar kwayoyi
DCP Abba Kyari a Majalisar Tarayya @HouseNgr
Asali: UGC

A ranar guda:
☑️ NDLEA ta na neman Abba Kyari da hannu kan harkar kilo 25 na hodar iblis
☑️ ASUU ta tafi yajin-aiki
☑️ ASUU ta ce Farfesan da aka ba Isa Pantami' ya saba doka
Yaushe za a bude shafin Youtube a kan Najeriya?

- Adewale Adetona

Hukumar PSC da AGF Abubakar Malami su na da hannu a badakalar Abba Kyari. Ana neman Kyari a Amurka, an dakatar da shi daga aiki, yana harkar kwaya. Amma ana cigaba da lallabarsa. Bari mu ga yadda NDLEA za ta bullowa wannan lamarin.

- Frist Lady Ship

Badakalar Abba Kyari za ta tona asiirin wasu da yawa. Za a bankado mutanenku. Akwai sauran jan-aiki.

- FS Yusuf

Haka za a gaji a hakura

NDLEA ta na wasa da hankalin mutane ne. Ko ni da ba na aikin damara, na san inda za a kama Abba Kyari idan ana namensa. Sun san inda yake, idan da gaske suke.

Kara karanta wannan

Cikakken bayani: 'Yan sanda sun bi Abba Kyari da wasu mutane, sun kwamushe su

- The Bri Deb

Kamar dai Ogbeni Dipo, First Lady Ship da John Odey yana ganin babu abin da zai faru da Abba Kyari in dai Najeriya ce, za a bada belinsa ne kurum sai maganar ta mutu.
Abba Kyari – Zai kai kan shi gaban NDLEA yau ko gobe. Za a tsare shi, daga nan a bada belinsa a mako mai zuwa. A karbe masa fasfo kamar yadda sharadin belin zai bukata, a hana shi fita kasar waje domin shari’ar da ba za a taba yi ba.

- Joe Odey

NDLEA ta fitar da sanarwa

Asali: Legit.ng

Online view pixel