TY Shaban ya gasgata maganar Naziru, ya bukaci ya rantse bai taba neman wata jaruma da lalata ba

TY Shaban ya gasgata maganar Naziru, ya bukaci ya rantse bai taba neman wata jaruma da lalata ba

  • Jarumi kuma mawaki, TY Shaban ya fito inda ya saki wani bidiyo tare da gasgata batun Naziru Sarkin waka na cewa ana neman jarumai mata kafin a saka su fim
  • Sai dai Shaban ya kalubalanci fitaccen mawakin da ya fito ya yi ranstuwar cewa bai taba neman wata jaruma mace a masana'antar ba a kan zai saka a waka ko fim
  • A makon da ya gabata ne masana'antar Kannywood ta rincabe kan zancen da Ladin Cima ta ce ba a biyan ta sama da dubu biyu zuwa dubu biyar a fim

Masana'antar Kannywood ta barke da rigima tun bayan ikirarin da Ladin Cimma ta yi na cewa ana biyanta dubu biyu zuwa dubu biyar idan ta yi fim.

Babban abunda ya sake hargitsa jaruman shi ne bidiyon da Naziru Sarkin wakan Kano ya fitar inda ya caccaki Ali Nuhu da Falalu A. Dorayi.

TY Shaban ya gasgata maganar Naziru, ya bukaci ya rantse bai taba neman wata jaruma da lalata ba
TY Shaban ya gasgata maganar Naziru, ya bukaci ya rantse bai taba neman wata jaruma da lalata ba. Hoto daga @official_tyshaban
Asali: Instagram

A cikin bidiyon ne ya kara da cewa wasu jaruman biya suke a saka su a fim yayin da ake lalata da wasu matan kafin a saka su a fim baki daya.

Wannan tonon silili da Sarki yayi yasa wasu mata daga masana’antar suka fito kai tsaye suka karyata batun da kuma ware kansu koda ana yi banda su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma kuma kwatsam sai TY Shaba ya fitar da bidiyo inda ya gaskata maganar sarkin waka amma kuma ya jefawa Sarkin Waka tambayar, idan zai iya rantsewa shi bai taba amfani da wata ba a masana’antar?

Duk da bata fuskarsa yayi a bidiyon, TY Shaba ya wallafa bidiyon a shafinsa, inda a cikin bidiyon ya nemi Sarkin Waka yayi rantsuwa bai taba neman wata kafin ya sata a waka ko fim ba, inda a kasa ya rubuta Kannywood dai ta mu ce, kowa ya gyara ya sani, kowa ya bata ya sani.

Kannywood: Batun biyan Ladin Cima dubu biyu a fim ya tada hazo a masana'antar

A wani labari na daban, mutane a shafukan sada zumunta sun dinga maganganu daban-daban kan ikirarin jaruma Ladin Cima na cewa wasu furdusoshi na biyan ta dubu biyu zuwa dubu biyar idan ta fito a fim din su.

BBC ta zanta da ita a shirin Daga Bakin Mai Ita, kuma Ladin Cima Haruna ta ce dalilinta na gaza mallakar gidan kan ta shi ne rashin samun kudi a dunkule wanda ya taba kai dubu ashirin, talatin ko hamsin a harkar fim.

Asali: Legit.ng

Online view pixel