Sheikh Gumi ya magantu kan gobarar da gidansa yayi, hotunan wurin sun bayyana

Sheikh Gumi ya magantu kan gobarar da gidansa yayi, hotunan wurin sun bayyana

  • Sheikh Ahmad Mahmud Gumi, fitaccen malamin addinin Islama da ke zama a Kaduna, ya bayyana gobarar da ta tashi a gidansa da kaddara daga Allah
  • A ranar Asabar ne gobara ta tasi a gidan fitaccen malamin inda ta lakume sashi daya na bene wanda ya hada da makarantar Islamiyyarsa
  • Sheikh Gumi ya bayyana cewa har a halin yanzu ba a san musabbabin gobarar ba domin kuwa babu wutar lantarki ko a lokacin da ta tashi

Fitaccen malamin addinin musulunci nan, Sheikh Ahmad Gumi ya siffanta gobarar da ta ci wani bangare na gidan shi da ikon Allah.

Ya kara da cewa har yanzu ba a san abinda ya haddasa gobarar ba, saboda lokacin da al'amarin ya auku babu wutar lantarki, Tribune Online ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Karin Bayani: Gobara Ta Tashi a Gidan Sheikh Ahmad Gumi a Kaduna

Da farko, wata majiya da ta roki a sakaya sunan ta, ta ce wutar ta fara ci ne a sashin makarantar Islamiyya.

Haka zalika, an ga bidoyon gobarar da aka wallafa a shafin sa na Facebook, inda samari suke kokarin ganin wutar bata shafi sauran bangarorin ginin ba.

Sheikh Gumi ya magantu kan gobarar da gidansa yayi, hotunan wurin sun bayyana
Sheikh Gumi ya magantu kan gobarar da gidansa yayi, hotunan wurin sun bayyana. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Gobara Ta Tashi a Gidan Sheikh Ahmad Gumi a Kaduna

A wani labari na daban, gobara ta tashi da gidan shahararren malamin addinin musulunci mazaunin Kaduna, Sheikh Ahmad Gumi a yau Asabar. Rahoton da Vanguard ta wallafa ya ce ana can ana kokarin kashe wutan duk da cewa ba a rasa rai ba.

'Yan jarida ba su samu cikakken bayani ba duba da cewa kowa ya mayar da hankali ne wurin kokarin kashe gobarar da kuma tabbatar da cewa babu wanda ya rasu sakamakon gobarar. Daily Trust ta rahoto cewa ana amfani da wani bangare na gidan a matsayin makaranta.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan fashi sun yi awon gaba da motar kudi, sun kashe 'yan sanda 2

Asali: Legit.ng

Online view pixel