Najeriya yanzu na rugujewa hannun jahilan Shugabanni, marasa hangen nesa, IBB

Najeriya yanzu na rugujewa hannun jahilan Shugabanni, marasa hangen nesa, IBB

  • Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya soki Shugabannin Najeriya dake mulki yanzu da rashin hangen nesa
  • Babangida ya yi kira ga yan Najeriya suyi amfani da damar 2023 wajen sauya tarihin siyasar Najeriya
  • Manyan jiga-jigan siyasa na cigaba da zuwa Minna wajen Babangida neman tabarruki

Tsohon Shugaban kasa na mulkin Soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya.), ya bayyana cewa Najeriya fa yanzu tana rugujewa hannun jahilan shugabanni.

A rahoton DailyTrust, Babangida yace masu rike da ragamar mulkin kasar yanzu yan kama karya ne, kidahumai, masu kabilanci kuma marasa kwarewa da hangen nesa.

Janar IBB
Najeriya yanzu na rugujewa hannun jahilan Shugabanni, marasa hangen nesa, IBB Hoto: Dino
Asali: Facebook

IBB ya bayyana hakan ne yayinda ya karbi bakuncin tawagar Shugabannin uwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), karkashin jagorancin Sanata Iyorcha Ayu, a gidansa dake Minna, jihar Neja.

Kara karanta wannan

2023: Hotunan ziyarar da manyan jiga-jigan PDP suka kaiwa tsohon shugaban kasa, IBB

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

IBB yace:

"Tun da mun gaza shawo kan siyasar jam'iyya tun bayan karban yanci, yanzu muna da daman sauya siyasar Najeriya zuwa ta jama'a, bisa doka ta 13 da 14 na kundin tsarin mulkin Najeriya."

Shugaban PDP, Iyorcia Ayu ya bayyana cewa sun kaiwa tsohon shugaban ziyara ne don neman albarkarsa da shawara a matsayinsa na uba kuma daya cikin mu'assasan PDP.

Zaben 2023: Duk jam'iyyar da ta tsayar da ɗan arewa ba zata samu nasara ba, Gwamnan APC

A wani labarin kuwa, shugaban ƙungiyar gwamnonin kudu kuma gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu (SAN), ya yi gargaɗin cewa duk jam'iyyar da ta tsayar da ɗan arewa a takarar shugaban ƙasa ba zata yi nasara ba.

Daily Trust ta rahoto cewa gwamnan ya yi wannan furucin ne a ofishinsa, yayin da ya karɓi baƙuncin kungiyar Power Rotation Movement, bisa jagorancin shugaba, Dakta Pogu Bitrus.

Kara karanta wannan

Ku nemi kujerun sanatoci, ku bar matasa su shugabanci kasar - Tsohon ministan Buhari ga Atiku da Tinubu

Akeredolu yace duk ma su nuna adawa da tsarin mulkin karɓa-karba to ba su ƙaunar Najeriya ta cigaba da zama ƙasa ɗaya kuma tsintsiya ɗaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel