ASUU za tayi zamanta na karshe yau, gobe za ta yanke shawara kan yajin aiki

ASUU za tayi zamanta na karshe yau, gobe za ta yanke shawara kan yajin aiki

  • Malaman jami'o'in Najeriya zasu yi zamansu ta karshe yau da gobe don yake shawara kan lamarin yajin aiki
  • Malamin jami'oi tuni sun bayyana cewa su fa sun fidda kauna da gwamnatin Shugaba Buhari
  • Idan suka tafi yajin, ba zasu dawo ba sai lokacin da ake biya dukkan bukatunsu, a cewarsu

Legas - Majalisar zartaswar kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ASUU za ta fara zaman kwanaki biyu a jami'ar Legas, Akoka ranar Asabar domin yanke shawara kan maganar yajin aikin sai baba ta gani.

ASUU za ta gudanar da zabe ne kan wannan shawara kuma a sanarwa al'umma ranar Lahadi, wani mamba majalisa ya bayyana jaridar Punch.

Yace:

"Ba shugaban kungiyarmu zai yanke shawara kan yajin aikinmu ba. Hakazalika ba wani dan majalsar zartaswa zai yanke shawara shi kadai ba. Za'a tattauna lamuran ne a zaman gana."

Kara karanta wannan

Borno: Gwamna Zulum ya yi magana kan takarar shugaban ƙasa karkashin APC a 2023

"Sannan sai a gudanar da zabe. Abinda muka yanke shawara ranar Lahadi shi za'a yi."

ASUU za tayi zamanta na karshe yau, gobe za ta yanke shawara kan yajin aiki
ASUU za tayi zamanta na karshe yau, gobe za ta yanke shawara kan yajin aiki
Asali: UGC

Zamu shiga yajin aiki, gwamnati ba tada alkawari: ASUU

Kungiyar ASUU a ranar Juma'a ta bayyana cewa zata shiga yajin aiki saboda gwamnatn Buhari bata shirya cika alkawuran da tayi mata ba.

ASUU ta siffanta abinda Gwamnatin tarayya ke yi matsayin abin kunya musamman kan na'urar IPPIS duk da hujjoji daga ofishin Odito-Janar cewa ba tada inganci.

A jawabin da ASUU ta saki ranar Juma'a, ta bayyana yadda Gwamnati ta ki aiwatar da shawarin da aka yanke a zaman ganawa daban-daban don inganta Ilimi a Najeriya.

Shugaban kungiyar ASUU, shiyar jami'ar Jos, Dr Lazarus Maigoro, ya rattafa hannu kan jawabin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel