Buhari, Gwamnoni da shugabanni ne zasu tsayar da ɗan takarar APC a 2023, Zulum

Buhari, Gwamnoni da shugabanni ne zasu tsayar da ɗan takarar APC a 2023, Zulum

  • Gwamna Babagana Umaru Zulum na jihar Borno ya bayyana hanyar da APC zata bi wajen tsayar da ɗan takarar shugaban kasa
  • Zulum yace APC zata dogara ne kacokan ga shawarar shugaban Buhari, gwamnoni da shugabannin jam'iyya na kowane mataki
  • A cewarsa za su yi iyakar bakin kokarin su wajen haɗa kan jam'iyyar APC da kuma nasararta don cigaban ƙasa

Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umaru Zulum, yace shugaba Buhari, gwamnoni da shugabannin jam'iyya ne ke da alhakin zakulo wanda zai kare mutuncin APC a 2023.

Vanguard ta rahoto Zulum na cewa APC zata dogara da hukuncin da waɗan nan mutanen suka yanke kan wanda ya dace ya fafata zaben shugaban ƙasa karkashin inuwar APC.

A cewar gwamnan, nuna sha'awar takara a zaben fidda gwani, ba zai hana jam'iyyar APC zaman sulhun fitar da ɗan takara ba, domin haɗa kai da kuma cigaban ƙasa.

Kara karanta wannan

2023: Abu ɗaya ya rage wa Shugaba Buhari wanda zai bar baya mai kyau, Tambuwal

Farfesa Babagana Umaru Zulum
Buhari, Gwamnoni da shugabanni ne zasu tsayar da ɗan takarar APC a 2023, Zulum Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Zulum ya yi wannan furucin ne yayin da yake jawabin maraba ga mambobin kungiyar PCG, waɗan da suka kai masa ziyara har Ofis ranar Jumu'a.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa zata yi aiki da yan majalisu, shugabannin jam'iyya na kowane mataki wajen tabbatar da an aiwatar da matakin da Buhari ya ɗauka.

Ina goyon bayan haɗin kai don cigaban ƙasa - Zulum

Zulum ya ce:

"Ina bayan duk wani yunkuri da zai kara haɗa kan jam'iyya da kawo cigaban Najeriya, a dai-dai wannan lokaci mai wahala, ba wanda zamu bari ko wani abu ya hana jam'iyya dunƙule wa."
"Mu zamu zakulo mutanen da ya dace su jagoranci ƙasar nan, kuma hakan na bukatar gwamnoni, masu ruwa da tsaki na jam'iyya da shugaba Buhari su yi aiki tare."
"Gwamnatin Borno karkashi na zata haɗa kai da kokarin tabbatar da APC ta yi nasara. Zamuyi aiki da masu ruwa da tsaki, yan majalisu da shugabannin jam'iyya, wajen cimma matsayar da zata ɗaga Najeriya."

Kara karanta wannan

Najeriya yanzu na rugujewa hannun jahilan Shugabanni, marasa hangen nesa, IBB

Dalilin zuwan PCG wurin Zulum

Mambobin kungiyar PCG dake goyon bayan mataimakin shugaban ƙasa sun gana da gwamna Zulum, Sakataren gwamnatin Borno, Alhaji Usman Jidda, da sauran yan majalisar zartarwa ta jihar.

Sun gana da yammacin Jumu'a da nufin isar da sakon haɗa kan jam'iyya wajen tsayar da mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo, takarar shugaban ƙasa.

A wani labarin kuma Hukumar jin dadin yan sanda ta faɗi mataki na gaba da ta ɗauka kan Abba Kyari

Hukumar jin dadin yan sanda PSC ta bayyana cewa a halin yanzun ta jinkirta ɗaukar mataki kan Abba Kyari sabida wasu dalilai.

Hukumar ta sanar da cewa zata jira har sai an kammala bincike, kuma ta baiwa yan sanda wa'adin mako biyu su kawo rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel