Mu hada kai don Tinubu ya zama Shugaban kasa, Gwamna Sanwo-Olu ga shugabannin APC

Mu hada kai don Tinubu ya zama Shugaban kasa, Gwamna Sanwo-Olu ga shugabannin APC

  • Gwamna Sanwo-Olu na Legas ya yi kira da al'ummar mazauna jihar su hada kai da su don Tinubu ya dane kujerar shugaban kasa
  • Jagoran APC, Bola Tinubu, ya bayyana niyyar takara kujeran shugabancin Najeriya a zaben 2023
  • Sanwo-Olu yace Tinubu abin alfahari ne ga al'ummar Legas kuma akwai bukatar ya wakilcesu a Abuja

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya yi kira ga shugabannin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) su hada kai da juna don Asiwaju Bola Tinibu, ya samu nasarar zama shugaban kasa.

Ya bayyana hakan ne yayinda ya kai ziyarar aiki karamar hukumar Amuwo-Odofin da karamar hukumar Oriade ranar Laraba, rahoton ChannelsTV.

A cewarsa, akwai bukatar su sadaukar da kansu don Tinubu ya zauna daram-dam a Abuja don mulki ta dawo hannun yankin Legas.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Masu son kujerar Buhari basu san dumin da ke tattara da ita ba, inji Sanusi

Yace:

"Ina kira gareku wannan gwagwarmaya da muka dauka na ganin cewa Asiwaju (Tinubu) ya wakilcemu a Abuja na nan tafe."
"Ina kira ga dukkan Sarakuanan gargajiya su hada kai da gwamnonin kananan hukumomi - Ina kira ga dukkan al'ummar Inyamurai, kudu da Arewa."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamna Sanwo-Olu
Mu hada kai don Tinubu ya zama Shugaban kasa, Gwamna Sanwo-Olu ga shugabannin APC
Asali: UGC

Asali: Legit.ng

Online view pixel