Mu zamu sake zaban wanda zai zama Gwamna a Taraba: Kungiyar CAN ta caccaki Musulmai

Mu zamu sake zaban wanda zai zama Gwamna a Taraba: Kungiyar CAN ta caccaki Musulmai

  • Shugaban kungiyar Kiristocin Najeriya na jihar Taraba ya yi raddi wa shugabannin majalisar Musulman jihar
  • Rabaran Magaji ya ce kungiyar Musulman su daina yada farfaganda don wanzuwar zaman lafiya a jihar
  • CAN ta ce Kiristoci ke da rinjaye a jihar saboda haka duk lokacin da akayi zabe wanda ta zaba zai lashe

Jalingo - Kungiyar Kiristocin Najeriya CAN a jihar Taraba ranar Alhamis ta bayyana cewa ita zata sake zaban wanda zai zama gwamnan Taraba saboda yawan mabiyanta.

Kungiyar ta caccaki majalisar Musulman jihar Taraba da kungiyar kare hakkin Musulmai MURIC bisa ikirarin da suke na cewa ana musgunawa Musulmai a jihar.

CAN tace ko Musulmai su yarda ko kada su yarda sune maras rinjaye a jihar kuma ba zasu taba nasara a zabe ba.

Kara karanta wannan

Rikicin APC a Kano: Dattawan jihar sun shiga tsakanin tsagin Ganduje da Shekarau

Kungiyar CAN ta caccaki Musulmai
Mu zamu sake zaban wanda ke zai zama Gwamna a Taraba: Kungiyar CAN ta caccaki Musulmai Hoto: DDR
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban CAN na jihar, Rabaran Isaiah Magaji, ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da manema labarai, rahoton Punch.

Yace tuhume-tuhume da majalisar Musulmi da MURIC ke yi karya da babatu ne, kawai suna son barazana ga Kiristocin jihar ne wanda sune mafi rinjaye.

Yace:

"Mu kungiar addini ne masu son zaman lafiya kuma ba zamu so mu biyewa yan'uwanmu Musulmai ba, amma wajibi ne su daina wannan farfagandan da suke kokarin yi kan gwamnan idan ana son zaman lafiya."
"Idan Sarkin Musulmi, Sarkin Muri, Alhaji Abbas Njida Tafida, zai jinjinawa Gwamna Ishaku kwanakin baya a Takun, me yasa majalisa Musulmai da MURIC suke wani magana daban?"

Mu ke da rinjaye a Taraba, kuma zamu iya yadda muka so, CAN

Rabaran Magaji ya kara da cewa kungiyar CAN na da ikon yin irin abinda Gwamna El-Rufa'i yayi a Kaduna na zaben mataimaki Musulmi amma suna hakuri da Musulmai don zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Kisan Hanifa: Aisha Buhari ta kai ziyarar ta'aziyya jihar Kano, ta yi jawabi mai ratsa zuciya

A cewarsa, kada Musulmai suyi tunanin sun yi hakan ne don tsoro.

Yace:

"Muna da rinjaye kuma duk inda Kirista suka kada kuri'a, nan za'a lashe zabe a Taraba. Da mun zabi yin irin abinda Shugaba Buhari keyi a tarayya da El-Rufa'i a Kaduna, amma muna hakuri da yan'uwanmu Musulmai."
"Kada a daukemu wawaye don muna da saukin kai."

CAN ta kara da cewa Gwamnatin Darius Ishaku ta baiwa Musulmi mukami masu muhimmanci kuma na yi hakan ne don sun cancanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel