Zaben 2023: Masu son kujerar Buhari basu san dumin da ke tattara da ita ba, inji Sanusi

Zaben 2023: Masu son kujerar Buhari basu san dumin da ke tattara da ita ba, inji Sanusi

  • Alhaji Muhammadu Sanusi II, tsohon Sarkin Kano, ya yi wasu muhimman bayanai game da kalubalen da Najeriya ke fuskanta
  • Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) yace baya sha'awar maye gurbin shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023
  • Sanusi ya aike da wani muhimmin sako ga masu zuba ido ga kujerar shugaban kasa a 2023, inda ya bayyana irin mutanen da yakamata a zaba

Abeokuta, jihar Ogun - Tsohon Sarkin Kano na 14, Alhaji Muhammadu Sanusi II, ya musanta cewa ya na neman dale kujerar shugaban kasa a 2023, yana mai cewa ya gamsu da kasancewarsa jagoran darikar Tijjaniyya.

Sanusi ya bayyana haka ne a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, yayin da yake amsa tambaya a wajen wani liyafar bikin cika shekaru 80 na Babanla Adinni na Egbaland, Cif Tayo Sowunmi, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Ka goyi bayan Tinubu: 'Yan Kudu sun nemi Osinbajo ya janye batun gaje kujerar Buhari

Sanusi Lamido Sanusi kan batun maye gurbin Buhari
Zaben 2023: Masu son kujerar Buhari basu san dumin da ke tattara da ita ba, inji Sanusi | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Sanusi, tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa ya yi ayyuka daban-daban a da da kuma yanzu kuma zai "kasance mai godiya ga Allah har abada.”

Shugaban na darikar Tijjaniyya a Najeriya ya kuma gargadi masu neman shugabancin kasar nan a 2023 da su kasance cikin shiri domin gudanar da babban aiki bayan gaje kujerar Buhari.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Najeriya za ta fuskanci kalubale mai zurfi nan gaba – Sanusi

A yayin jawabinsa, Sanusi ya kuma bayyana cewa Najeriya "tana rayuwa ne a yanzu kan karin lokaci."

Ya ce kasar za ta fuskanci kalubale masu zurfi daga 2023.

Kalamansa:

“A gaskiya, muna rayuwa ne akan karin lokaci. A 2015, mun kasance a cikin wani rami mai zurfi. A 2023 ma, za mu kasance cikin rami mai zurfi fiye da na 2015.
“Kalubalan da ke gaban dukkan mutanen da ke son zama shugaban kasa, ina fatan za su fahimci cewa matsalolin da za su fuskanta iri-iri ne kamar matsalolin da aka fuskanta a shekarar 2015 kuma dukkanmu mu kasance a shirye don fuskantar tsauraran matakai masu wahala kuma idan an dauke su, dukkanmu za mu dandana."

Kara karanta wannan

Ya kamata PDP ta karɓe mulkin Najeriya, zaman lafiya ya gagara, inji gwamnan PDP

Ka goyi bayan Tinubu: 'Yan Kudu sun nemi Osinbajo ya janye batun gaje kujerar Buhari

An bukaci mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osibanjo da ya janye aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa tare da yin gangami wajen ganin Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa a 2023.

Wani shugaban matasa a yankin Neja Delta, Mista John Dekawei ne ya yi wannan kira a Warri yayin zantawa da manema labarai.

Ya ce ya kamata Farfesa Osibanjo ya kasance mai biyayya ga jagoran siyasarsa,wato Tinubu ta hanyar mara wa takararsa ta shugaban kasa baya, inji rahoton Vanguard.

A wani labarin na daban kuma Gwamna Yahaya Bello ya faɗi lokacin da zai bayyana kudirin takarar shugaban ƙasa a 2023.

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi, yace babu tantama zai amsa kiran da yan Najeriya maza da mata, dake sassan duniya ke masa.

Bello, ya sanar wa masoyansa dake fadin kasa cewa a halin yanzun ya maida hankali kan babban taron APC, amma da an kammala zai amsa kiran su.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Okorocha ya gana da Buhari kan kudirinsa na son zama magajinsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel