Batanci ga Annabi: Sharif-Aminu ya bukaci kotu tayi watsi da karar da aka shigar kansa

Batanci ga Annabi: Sharif-Aminu ya bukaci kotu tayi watsi da karar da aka shigar kansa

  • Matashin da ake zargi da batanci kan Annabi, Sharif-Aminu ya bukaci kotun daukaka kara tayi watsi da karar da gwamnatin Kano ta shigar kansa
  • Sharif-Aminu hakazalika ya bukaci kotun tayi watsi da dokar shari'ar Musulunci saboda ta sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya
  • Yau ranar Alhamis kotun daukaka kara zata saurari karar Sharif-Aminu

Kano - Mawakin bege, Yahaya Sharif-Aminu, wanda aka yiwa zargin batanci ga Annabi (SAW) ya bukaci kotun daukaka kara ta hana sake gurfanar da shi kan laifin batanci.

PremiumTimes ta ruwaito cewa Lauyansa, Kola Alapinni, ya bayyana cewa kotun daukaka kara dake Kano ta zabi ranar Alhamis (Yau) domin sauraron karar.

Lauyan ya kara da cewa Gwamnatin jihar Kano har yanzu basuyi martani kan bukatar Yahaya Sharif-Aminu ba.

Ana kyautata zaton cewa sakamakon rashin martanin Gwamnatin Kano, za'a baiwa kotu daman yanke hukunci yau (Alhamis).

Kara karanta wannan

Almundahanar kudin makamai N13.8bn: An hana tsohon shugaban Soji fita kasar waje

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sharif-Aminu
Batanci ga Annabi: Sharif-Aminu ya bukaci kotu tayi watsi da karar da aka shigar kansa
Asali: Facebook

Ba zai sake gurfana gaban kotu ba

Lauyan Sharin Aminu ya bukaci kotun daukaka karar tayi watsi da shari'ar babbar kotun jihar ta da tace a sake gurfanar da shi. Yace kawai yanzu a wankesa daga laifin kuma a sakesa.

Hakazalika ya yi kira ga kotun daukaka kara ta yi watsi da dokar Shari'ar Musulunci na jihar Kano saboda ta sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel