Surukata ce ta hure wa matata kunne, Magidanci da ke neman kotu ta datse igiyar aurensa

Surukata ce ta hure wa matata kunne, Magidanci da ke neman kotu ta datse igiyar aurensa

  • Wani magidanci ya garzaya kotu inda ya nemi a datse igiyar aurensa kan dalilin cewa surukarsa ta lalata masa aure
  • Mr Uchenna Okolie ya shaidawa kotu cewa tun bayan da ya rasa aikinsa, surukunsa ta fara fushi da shi tana masa masifa duk lokacin da ta zo gidansa
  • Ya ce daga bisani surukar ta zuga matar sun kwashe kayansa da yaransa sun tafi kuma har yanzu ba su dawo ba

FCT, Abuja - Wani dan kasuwa, Mr Uchenna Okolie, a ranar Alhamis, ya roki wata kotun kwastamare da ke zamanta Jikwoyi ta raba aurensa kan dalilin cewa surukarsa ta lalata masa auren.

Mutumin da ya yi karar, mazaunin Abuja ya bayyana hakan ne cikin takardar karar da ya shigar kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mota dauke da silindar gas ta fadi a Kano, ta lalata kayayyaki, ta yi kisa

Surukata ce ta hure wa matata kunne, Magidanci da ke neman kotu ta datse igiyar aurensa
Surukata ce ke zuga matata, mai gida ya nemi kotu ta raba aurensa. Hoto: Vanguard

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Suruka ta ta lalata min aure. Ta na da yawan masifa kuma ta ki jini na tun bayan da na rasa aiki na.
"Duk lokacin da ta zo gida domin taimakawa mata na da ta haihu, sai ta rika saka ni aiki. Duk abin da na aikata domin in faranta mata rai sai ya fusata ta. Duk lokacin da ta zo gida na, babu zaman lafiya," in ji shi.

Surukata ta ta hure wa matata kunne

Mai shigar da karar ya kuma shaida wa kotu cewa surukarsa ta hure wa matarsa kunne.

"Suruka ta a ko da yaushe tana haddasa fitina tsakani na da matata.
"Na bar gidan bayan wani rikici da muka yi kuma da na dawo da yamma, na tarar ta tattara komai a gida na ta tafi da shi har da mata na da yara na.

Kara karanta wannan

Bawan Allah ya yi wa Hadiza Gabon zagin cin mutunci, ta yi masa martani da kyakyawar addu'a

"Tun lokacin na yi kokarin dawo da mata ta amma abin ya ci tura.
"A dalilin hakan ne yasa na ke son a raba auren mu da matata, kuma ina son a bani yara na biyu," a cewarsa.

Wacce aka yi karar ta, Ijeoma, wacce matar aure ce, bata halarci zaman kotun ba kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Alkalin kotun, Labaran Gusau, ya dage cigaba da shari'ar zuwa ranar 28 ga watan Fabrairun shekarar 2022.

A raba mu, ya ce na cika mugun ci, har rufe kicin yake yi da dare, Firdausi ta yi karar mijinta Haruna a kotu

A wani labarin daban, wata Firdausi Sulaiman mai shekaru 23 ta maka mijin ta, Haruna Haruna a gaban kotun musulunci da ke zama a Magajin Gari a Kaduna tana bukatar a raba auren su da shi saboda yadda yake dukanta kamar gangar tashe sakamakon mungun cin abincin ta.

Kara karanta wannan

Kannywood: Isa ya yi martani kan hukuncin da kotu ta yankewa Sadiya Haruna kan batancin da ta yi masa

Kamar yadda NewsWireNGR ta bayyana, a korafin da ta yi wa Kotu, Firdausi wacce take zama a Rigasa dake Kaduna ta ce har rufe kicin Haruna yake yi da dare.

Alkalin kotun, Nuhu Falalu, bayan sauraron bangarorin guda biyu, ya dage sauraron shari’ar har sai ranar 4 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel