Innalillahi: Mota dauke da silindar gas ta fadi a Kano, ta lalata kayayyaki, ta yi kisa

Innalillahi: Mota dauke da silindar gas ta fadi a Kano, ta lalata kayayyaki, ta yi kisa

  • Hukumar kashe gobara a jihar Kano ta tabbatar da faruwar wani hadari, inda wani mutum ya mutu nan take
  • Wata mota mai dauke da iskar gas ta fadi, inda ta rutsa da wasu mutane biyu daya ya mutu, yayin da aka ceto dayan
  • Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta yi kira ga direbobi da suke kulawa da natsuwa yayin da suke tukin mota

Jihar Kano - Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutum daya a wata fashewar da aka samu ta iskar gas da ta afku a kauyen Ijarawa da ke karamar hukumar Bichi a jihar.

Rahoton da jaridar Punch ya bayyana cewa, wani mutum daya ya tsira daga lamarin.

Hadarin mota ya hallaka mutane a Kano
Innalillahi: Mota dauke da silindar gas ta fadi a Kano, ta lalata kayayyaki, ta yi kisa | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara, Alhaji Saminu Abdullahi ya fitar ranar Litinin a Kano, inda ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da safiyar yau 8 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Ba na son cin haram, ana biya na kudin da ban yi aiki ba, Hadimin gwamna ya yi murabus

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Mun samu kiran gaggawa daga Insifeto Daiyabu Tukur da misalin karfe 07:46 na safe cewa wata mota da ke dauke da silindar gas din girki ta fadi a kan titi kuma daya daga cikin kayan ya fashe.
"Bayan samun labarin, mun aika da tawagarmu cikin gaggawa zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 8:00 na safe domin ceto wadanda abin ya rutsa dasu."

Ya ce motar J5 mai lamba FB 52 LAD ta kasuwanci ce ta dauko kayayyakin gas din zuwa Katsina daga Kano.

Abdullahi ya ce hatsarin ya rutsa da mutane biyu, Maikano Muhammad dan shekaru 45, wanda ya mutu nan take, yayin da Abdullahi Usman dan shekaru 40, shi kuma aka ce to shi.

Ya kara da cewa:

“Dukkan wadanda abin ya rutsa dasu an mika su ga ofishin 'yan sanda na Usman Usman da ke a Bichi.

Kara karanta wannan

An kashe ma'aikaciyar FIRS ranar da aka shirya bikin yi mata ƙarin girma a ofis a Legas

"Ana ci gaba da bincikar musabbabin lamarin."

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ya yi kira ga direbobin da ke jigilar irin wadannan kayayyaki da su yi taka-tsan-tsan wajen daukar kaya tare da yin tuki cikin kulawa da natsuwa domin gujewa afkuwar hadurra akan tituna.

Gobara ta yi kaca-kaca da katafaren kamfani a jihar Kano

Gobara ta kone wani katafaren kamfanin kera ababen katako da ke Kano mai suna Alibert Furniture.

Daily Nigerian ta tattaro cewa gobarar ta tashi ne da sanyin safiyar yau Litinin, inda ta kone kamfanin da ke kan hanyar Murtala Mohammed a cikin babban birnin kasar.

An tattaro cewa jami’an tsaro biyu na kamfanin sun samu raunuka daban-daban kuma an garzaya da su asibiti.

Duk da cewa har yanzu ba a gano musabbabin tashin gobarar ba, shaidu sun alakanta gobarar da matsalar wutar lantarki da ta samu daga taransifomar kamfanin.

A wani labarin, an samu hargitsi a ranar Laraba, 3 ga watan Nuwamba, yayin da wata gagarumar gobara ta cinye wasu gine-gine da shaguna a Owode Onirin, daura da unguwar Ikorodu Road a Legas.

Kara karanta wannan

Kisan gilla: Bayan kisan Hanifa, wani Malami ya kashe Almajirinsa a jihar Kano

Vanguard ta rahoto cewa a lokacin da jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Legas, suka isa wurin da lamarin ya faru, wasu fusatattun matasa sun far musu.

An ce matasan sun kai wa jami’an hari ne saboda rahotanni sun ce sun isa wurin a makare bayan an yi ta kiran su yayin da wutar ta kama.

Asali: Legit.ng

Online view pixel