Kannywood: Isa ya yi martani kan hukuncin da kotu ta yankewa Sadiya Haruna kan batancin da ta yi masa

Kannywood: Isa ya yi martani kan hukuncin da kotu ta yankewa Sadiya Haruna kan batancin da ta yi masa

  • Jarumin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Isa A. Isa, ya yi martani akan daure Sadiya Haruna da kotu ta yi
  • Isa ya ce Allah ne ya tabbatar da gaskiyarsa shiyasa kotu ta daure jarumar na wata shida bayan ta same ta da hannu dumu-dumu a tuhumar da ake mata na masa batanci
  • Ya kuma ce tun farko abun da ya hadasa da jarumar taimako ne sabanin kazafin da tayi masa na cewa sun yi auren mutu'a da shi

Fitaccen jarumi kuma furodusa na masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Isa A. Isa, ya yi martani a kan hukuncin da kotu ta yankewa Sadiya Haruna.

Tun farko dai Isa ne ya shigar da kara kotu bisa bata masa suna da yake zargin jarumar kuma mai kayan mata tayi masa.

Kara karanta wannan

Gaskiya 6 da ya kamata ku sani game da Jaruma Sadiya Haruna da Kotu ta ɗaure

Jarumin ya ce Allah ne ya tabbatar da gaskiyarsa shiyasa kotu ta hukunta Sadiya bayan samunta da laifin abun da ake zarginta a kai.

Kannywood: Isa ya yi martani kan hukuncin da kotu ta yankewa Sadiya Haruna kan batancin da ta yi masa
Kannywood: Isa ya yi martani kan hukuncin da kotu ta yankewa Sadiya Haruna kan batancin da ta yi masa Hoto: @sadiyaharuna
Asali: Instagram

A hira da yayi da muryar Amurka, furodusan ya ce Sadiya ta kira shi da dan luwadi alhalin shi bai taba aikata hakan ba.

Ya ce:

“Yau kimanin shekara biyu da wata uku da yan kwanaki, wannan shari’ar ce dai take ta tafiya ake ta janta har Allah ya kawo ta yau ranar Litinin, 7 ga watan Fabrairu. Shine Allah ya tabbatar da hukuncinsa, ya tabbatar da mai gaskiya, ya kuma baiwa kowa gaskiyarsa.
“Kotu ta kamata da laifi, tayi mata sassauci, tayi mata daurin wata shida babu tara a gidan yari akan sharri da tayi mun, tayi mun kazafin abun da ban san shi ba.”

Kara karanta wannan

Da duminsa: Kotu ta yanke wa Jaruma Sadiya Haruna hukuncin wata 6 a gidan yari

Da aka tambaye shi kan sharri da kazafi da tayi masa, Isa ya ce:

“Duk wanda ke soshiyal midiya a Najeriya da ma duniya, ya ga cewa a shekara biyu da kamar wata hudu ya ga lokacin da wannan yarinyar Sadiya ta shiga soshiyal midiya ta yi mun kazafi na neman maza, ta yi mun kazafi dai na batanci da cin mutunci wanda a rayuwata ban san da shi ba.
“Toh a kan wannan ne na garzaya kotu ban dau hukunci a hannuna ba, na roki Allah ya zaba mun abun da yafi alkhairi, sai Allah ya tura ni kotun duniya tun kafin mu je nasa."

Dangane da alakar da ke tsakaninsa da Sadiya kafin ta yi masa batancin, sai ya ce:

“Kafin ta yi mun wannan kazafin alaka ce ta taimako. Ta zo gurina a kan in taimake ta, kuma Allah yasa bana wulakanta mutane. Ta ce ita masoyayita ce a harkar fim kuma ta shiga harkar an cuce ta na taimaketa don ta ji labarina ni mutumin kirki ne.

Kara karanta wannan

Wani Saurayi ya lakadawa budurwarsa duka har ta mutu bayan ya dirka mata ciki

“Na sa ta kawo mun fim din, na gyara shi, nasa aka raba shi gidajen talbijin domin ta samu abun kanta. Daga nan ne ta sa ni na zama babanta bata da kowa.
“Don na hana ta yin abubuwa da take yi a soshiyal midiya na batanci cewa ni zan rabu da ita idan bata daina ba. Wannan bakin cikin na rabu da ita ne yasa take bina da sharri."

Game da auren ‘mutu’a’ da jarumar ta ce sun yi, Isa ya ce karya take yi, shi bai aureta ba, bai ma san ya ake yin wannan auren ba.

Kotu ta yanke wa Jaruma Sadiya Haruna hukuncin wata 6 a gidan yari

A baya mun ji cewa kotu ta yanke wa jarumar Kannywood kuma mai siyar da kayan mata da maza, mai suna Sadiya Haruna hukuncin zaman wata shida a gidan yari ba tare da zabin tara ba.

Kara karanta wannan

An kama wata mata a Kano tana yunƙurin sace yaro ɗan shekara 5 a hanyarsa ta zuwa makaranta

An samu Sadiyan da laifin bata sunan wani jarumi kuma mawakin kannywood mai suna Isa A Isa, Sahelian Times ta ruwaito.

An gurfanar da wacce ake zargin ne akan laifin bacin suna wanda yaci karo da sashi ma 391 na Penal Code kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel