Gombe: An harbi wani soja yayin da yake ƙoƙarin daƙile harin da aka kai wani gari

Gombe: An harbi wani soja yayin da yake ƙoƙarin daƙile harin da aka kai wani gari

  • Wani soja ya samu mummunan rauni yayin da ya ke kokarin dakatar da wani hari da aka kai garin Nyuwar da ke Jihar Gombe wanda ya fara aukuwa tun ranar Talata
  • Ganau daga garin sun bayyana yadda harin ya kazanta har ya kai ga mutane suna tserewa garuruwa masu makwabtaka da Nyuwar don tsira
  • Makamancin harin ya taba aukuwa a watan Afirilun da ta gabata wanda ya mamaye garin Nyuwar da Jessu kamar yadda mutane da dama suka tabbatar

Gombe - Garuruwan da ke tsakanin Jihar Gombe da Jihar Adamawa a arewa maso gabashin kasar nan, sun rikice bayan wani rikicin ya afka garin Nyuwar da ke Jihar Gombe, ThisDay ta ruwaito.

Rikicin ya ci gaba da faruwa tun ranar Talata da rana bayan an harbi wani soja wanda ya yi kokarin dakatar da harin da aka kai garin Nyuwar da ke kusa da garin Waja.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Mota dauke da silindar gas ta fadi a Kano, ta lalata kayayyaki, ta yi kisa

Gombe: An harbi wani soja yayin da yake ƙoƙarin daƙile harin da aka kai wani gari
An harbi wani soja yayin ƙoƙarin daƙile harin da aka kai wani gari a Gombe. Hoto: ThisDay
Asali: Twitter

Ganau daga Nyuwar sun bayyana wa manema labarai a Gombe ta wayar salula cewa an ji wa wani soja rauni yayin dakatar da harin da aka kai garin kamar yadda aka taba yi a Nyuwar da Jessu a watan Afirilun shekarar da ta gabata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An zarce da sojan asibiti take-yanke

ThisDay ta tattaro bayanai akan yadda aka zarce da sojan zuwa wani asibiti yayin da harin ya ci gaba da aukuwa inda maharan suka zarce yawan jami’an tsaro.

Har gidaje da dama aka kai wa hari yayin da mata da yara suka dinga guduwa wasu garuruwan don neman tsira.

A Jessu, wani gari da ke da makwabtaka da Nyuwar, mutane da dama sun dinga guduwa daga garin saboda tsoron kada rikicin ya ritsa da su.

Ba wannan bane karon farko

Kara karanta wannan

Kaduna: Jami'an tsaro sun ragargaji 'yan bindiga, sun kubutar da wadanda aka sace

A watan Afirilun da ya gabata ne muten Waja suka kai hari garin Nyuwar da Jessu wanda ya ja mutane suka bar garuruwan zuwa makwabtan su.

Manema labarai sun so jin ta bakin jami’ar hulda da jama’an yan sandan yankin, Mary Obed Malum amma abin ya ci tura, don bata daga waya ba kuma bata kira ba.

A lokacin rubuta rahoton nan, kwamishinan labaran jihar, Julius Ishaya Lapes ya sanar da wakilin ThisDay cewa yana ta bincike ne don gano tushen rigimar. Kuma ya yi alkawarin tuntubar sa idan ya samu bayanai.

'Yan bindiga sun afka wa mutane a kan titi a Kaduna, sun kashe shida

A wani labarin, wasu da ake zargin makiyaya fulani ne sun kai wa mutane da ke tafiya a hanya hari a gaban Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Kagoro, Karamar Hukumar Kaura ta Jihar Kaduna.

Wani ganau, wanda ya tabbatar wa The Punch rahoton a ranar Alhamis, ya ce yan bindiga sun taho ne a kan babura sannan suka far wa wadanda suka gani.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan ta'adda sun sace limamin cocin katolika, sun sheke kukunsa

Ya ce mutane shida ne aka tabbatar sun rasu sakamakon harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel