Duk da rufe makarantu, har yanzu ana cigaba da zanga-zanga kan Hijabi

Duk da rufe makarantu, har yanzu ana cigaba da zanga-zanga kan Hijabi

  • Dalibai mata masu Hijabi a kasar Indiya na cigaba da zanga-zanga kan yunkurin hanasu shiga aji da Hijabi
  • An kulle Makarantun Sakandare a kudancin kasar Indiya biyo bayan zanga-zangan ranar Lahadi
  • Matasan addinin Hindu na cin mutuncin duk daliba macen da suka gani tana sanye da hijabi

Indiya - Duk da rufe makarantu, har yanzu ana cigaba da zanga-zanga kan hana mata Musulmi saka Hijabi a wasu makarantu a jihar Karnataka da ke kudancin Indiya.

Hukumomi a kudancin Indiya sun bada umurnin rufe makarantu ranar Talata yayinda zanga-zanga ya barke kan hana dalibai mata Musulmai shiga aji da Hijabi.

Rikicin wanda ya barke a jihar Karnataka ya tada hankulan jama'a saboda cin zarafin da yan addinin Hindu ke yiwa Musulmai karkashin mulkin Firai Minista Narenda Modi.

Kara karanta wannan

An rufe makarantu a Indiya sakamakon rikicin hana dalibai sanya Hijabi

Bayan Zanga-zangan ranar Talata da yayi munin da sai da jami'an tsaro suka tarwatsa mutane da hayakin yaji,an cigaba ranar Laraba, rahoton BBC.

Wannan ya biyo bayan sanarwar Ministan yankin Basavaraj Bommaina a rufe dukkan makarantun sakandaren jihar na tsawon kwanaki uku.

Hijabi
Duk da rufe makarantu, har yanzu ana cigaba da zanga-zanga kan Hijabi Hoto
Asali: Facebook

Duk da rufe makarantu, har yanzu ana cigaba da zanga-zanga kan Hijabi
Duk da rufe makarantu, har yanzu ana cigaba da zanga-zanga kan Hijabi
Asali: Facebook

Duk da rufe makarantu, har yanzu ana cigaba da zanga-zanga kan Hijabi
Duk da rufe makarantu, har yanzu ana cigaba da zanga-zanga kan Hijabi
Asali: Facebook

Duk da rufe makarantu, har yanzu ana cigaba da zanga-zanga kan Hijabi
Duk da rufe makarantu, har yanzu ana cigaba da zanga-zanga kan Hijabi
Asali: Facebook

Me ya haddasa zanga-zanga

A watan Junairu, wasu dalibai mata a makarantar gwamnati sun bayyana cewa an hanasu shiga aji zana jarabawa saboda sun sanya Hijabi.

Wannan abu ya yadu zuwa wasu makarantun inda aka fara samun fito-na-fito tsakanin dalibai Musulmai da na mabiya addinin Hindu.

Bidiyon wata daliba ya shahara a kafafen ra'ayi da sada zumunta inda mabiya addinin Hindu suke mata ihu don ta sanya Hijabi.

Ita kuwa dalibar ba tsoro ta fuskancesu tana fadin 'Allahu Akbar'

Kara karanta wannan

Almundahanar kudin makamai N13.8bn: An hana tsohon shugaban Soji fita kasar waje

Kalli bidiyon:

Asali: Legit.ng

Online view pixel