Wanda ICPC ta ke zargi da laifin satar Naira miliyan 900 yana so ayi sulhu a wajen kotu

Wanda ICPC ta ke zargi da laifin satar Naira miliyan 900 yana so ayi sulhu a wajen kotu

  • Lauyan da yake kokarin wanke Dibu Ojerinde ya nemi alfarmar a karasa shari’arsu a wajen kotu
  • A 2021 hukumar ICPC ta maka Ojerinde a gaban kotu a garin Abuja, ana zarginsa da wawurar N900m
  • Idan aka kama tsohon shugaban na NECO da JAMB da wannan laifi, zai iya shafe shekaru a daure

Abuja - Tsohon shugaban hukumar JAMB ta kasa, Dibu Ojerinde, ya na tunanin ya nemi alfarma a shari’ar da ake yi da shi a babban kotun tarayya a Abuja.

Wani rahoto da ya fito daga Premium Times a ranar Talatar nan ya bayyana cewa babban lauyan Dibu Ojerinde watau Ibrahim Ishyaku ya bayyana wannan.

Ishyaku SAN ya sanar da Alkali cewa za su tattauna a kan yadda za a warware matsalar a wajen kotu.

Kara karanta wannan

Ronaldo, Ozil, Mane da sauran ‘Yan kwallon kafa da suka fi kowa taimakawa marasa karfi

Punce ta ce Ibrahim Ishyaku SAN ya roki mai shari’a Obiora Egwuatu ya ba su kwana daya domin su zauna da hukumar ICPC da ke tuhumar wanda ake kara.

Babban lauyan ya fadawa Alkali cewa za a iya cigaba da shari’ar nan da sa’o’i 24 idan har an gagara samun matsaya tsakanin wanda yake karewa da ICPC.

ICPC Abuja
Hedikwatar Hukumar ICPC a Abuja Hoto: @icpcnigeria1
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lauyan ICPC ya sallama

Lauyan da ya shigar da wannan kara a madadin hukumar ICPC, Ebenezer Sogunle, bai nuna adawarsa ga wannan bukata da takwaran na sa ya bijiro da shi ba.

Kamar yadda mu ka samu labari, Obiora Egwuatu ya karbi wannan roko, inda ya bukaci ayi zama a ranar Laraba, 9 ga watan Fubrairu 2022 domin a saurari shari'ar.

A irin wannan tsari na neman sulhu a wajen kotu, za a yi wa wanda ake tuhuma da laifi sassaucin hukuncin saboda ganin ya ragewa Alkali wahalar aiki.

Kara karanta wannan

Kisan gilla: Bayan kisan Hanifa, wani Malami ya kashe Almajirinsa a jihar Kano

Zargin da ke wuyan Ojerinde

Tun a 2021 aka gurfanar da tsohon shugaban na hukumar JAMB bisa zargin ya saci N900m a lokacin da yake rike da hukumomin jarrabawan JAMB da NECO.

Ojerinde ya yi ikirarin cewa bai amsa laifin da ake zarginsa da aikatawa ba, don haka aka bada belinsa. Tun 2020 dai ICPC ta karbe wasu daga cikin kadarorinsa.

ASUU za ta shiga yajin-aiki?

Yayin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Malaman addini suke rokon ASUU su janye batun yajin-aiki, an ji cewa malaman Jami’a sun hau kujerar na-ki.

An shafe sama da shekara guda kenan gwamnati ba ta cika alkawarin da ta yi wa ASUU ba, don haka shugabanninta suka ce abin da ya rage shi ne a rufe makarantu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel