Mun shirya komawa wani sabon yajin-aikin da babu ranar dawowa inji 'Yan Kungiyar ASUU

Mun shirya komawa wani sabon yajin-aikin da babu ranar dawowa inji 'Yan Kungiyar ASUU

  • Kungiyar ASUU ta na iya komawa yajin-aiki a sakamakon rashin cika alkawarin gwamnatin tarayya
  • Shugabannin ASUU na rassa su na zargin gwamnatin Buhari da watsi da yarjejeniyar da aka cin ma
  • A karshen makon nan za a kira taron NEC inda ASUU za ta dauki mataki a kan batun yajin-aikin

Osun - Kungiyar ASUU ta malaman jami’a ta ce ‘ya ‘yanta su na shirin shiga wani danyen yajin-aiki, idan gwamnatin tarayya ba ta biya mata bukatunta ba.

Jaridar Punch ta rahoto ASUU ta reshen jami’ar fasaha ta Ladoke Akintola da ke garin Ogbomoso, jihar Osun ta na zargin gwamnatin kasar da rashin cika alkawura.

Shugaban ASUU da sakatarensa na jami’ar; Dr. Biodun Olaniran da Dr. Toyin Abegunrin sun fitar da jawabi bayan babban taron da aka yi na ranar Litinin da ta wuce.

Kara karanta wannan

Kaduna: Jami'an tsaro sun ragargaji 'yan bindiga, sun kubutar da wadanda aka sace

Kungiyar malaman jami’an ta nuna a shirye ta ke ta rufe jami’o’i har sai Illa – Mashaa Allahu, muddin gwamnati ba ta cika alkawuran da ta sa hannu da kanta ba.

Dr. Olaniran da Dr. Abegunrin sun yi kira ga al’umma su yi kokari wajen jan hankalin gwamnatin tarayya domin ta dauki matakin da ya dace tun kafin lokaci ya kure.

An kyale Ministoci da MoU

Shi ma shugaban ASUU na reshen jami’ar jihar Kwara da ke garin Malete, Dr. Salau Sheu ya shaidawa Punch cewa gwamnati na neman gujewa nauyin da ke kanta.

Kungiyar ASUU
Buhari ya zama Dakta a KASU Hoto: www.myschoolgist.com
Asali: UGC

A cewar Dr. Salau Sheu, gwamnatin Muhammadu Buhari ta bada umarni ga Ministoci su tabbatar da cewa an dabbaka yarjejeniyar MOU da aka cin ma a shekarar 2020.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: ASUU ta ce ba karatu ranar Litinin a BUK, za a tara dalilai da iyaye a yi musu bayani

Shugaban na ASUU ya ce wannan mataki da gwamnati ta dauka na barin aikin a kan wasu Ministoci biyu ba daidai ba ne domin ba da su aka yi tattaunawar ba.

Za a kira taron NEC

A ranar 12 da 13 ga watan Fubrairun 2022 ne kungiyar ta ASUU za tayi zaman majalisar koli a jami’ar Legas, inda za a dauki matsayar karshe a kan batun yajin-aikin.

Halin da ake ciki yanzu shi ne malamai ba su shiga aji a jami’o’i da-dama ba a ranar Litinin dinnan.

A Jami’o’in ABU Zaria, Unilorin, Uni Ben, Unizik da jami’ar Gombe, ‘yan ASUU sun ki shiga aji, inda suka buge da wayar da kan al’umma kan gwagwarmayar da suke yi.

Ba yau aka fara ba

Tun a karshen shekarar da ta gabata aka ji kungiyar ASUU ta na barazanar cewa idan ta tafi wani sabon yajin-aikin, babu ranar dawowa a kuma bude jami'o'in gwamnati.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Zamu shiga yajin aiki, gwamnati ba tada alkawari: ASUU

Shugaban ASUU na shiyyar Owerri, Uzo Onyebinama ya bayyana haka da ya zauna da ‘yan jarida. Onyebinama ya yi bayanin abin da ya sa suke tunanin sake rufe jami'o'in.

Asali: Legit.ng

Online view pixel