Bidiyo da Hotunan ziyarar jaje da Osinbajo ya kai wa iyayen Hanifa a Kano

Bidiyo da Hotunan ziyarar jaje da Osinbajo ya kai wa iyayen Hanifa a Kano

  • Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya kai ziyara gidan su Hanifa Abubakar, yarinyar da ake zargin mai makarantansu ya halaka ta
  • Mataimakin shugaban kasar ya kai ziyara Jihar Kano ne domin ya hallarci taron shekara-shekara ta mallamai masu koyar da masu koyon aikin lauya karo ta 53 inda ya ke babban bako
  • Osinbajo ya jajantawa iyayen Hanifa tare da nuna damuwa da rashin jin dadin abin da ya faru da yarsu yana mai kyautata zaton kotu za ta yi adalci a shari'ar

Kano - Farfesa Yemi Osinbajo, mataimakin shugaban kasar Najeriya ya ziyarci iyayen Hanifa Abubakar, yar shekara biyar da ake zargin malamin makarantarsu ya hada baki da wasu ya kashe ta, don yi musu ta'aziya.

Kara karanta wannan

Karar kwana: An shiga jimami yayin da matar tsohon mataimakin gwamna ta rasu

Farfesa Osinbajo ya kai ziyarar ne a ranar Talata 8 ga watan Fabrairu inda ya nuna damuwa da rashin jin dadi game da abin da ya faru da Hanifa.

"Bisa la'akari da iri jajircewa da jami'an tsaro suka yi wurin bincike, ina da tabbacin shari'a za ta yi wa wannan yarinyar da bata ji bata gani ba adalci," a cewar Osinbajo.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano da wasu ma'aikatan gwamnatin Jihar Kano sun yi wa Osinbajo rakiya yayin kai ziyarar.

Mataimakin shugaban kasar ya kai ziyara Jihar Kano ne domin ya hallarci taron shekara-shekara ta mallamai masu koyar da masu koyon aikin lauya karo ta 53 inda ya ke babban bako, rahoton Channels Television.

Ga hotunan a kasa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bidiyo da hotunan ziyarar da Osinbajo ya kai wa iyayen Hanifa a Kano
Osinbajo ya ziyarci iyayen Hanifa a Kano don yi musu jaje. Hoto: Tolani Alli
Asali: Twitter

Bidiyo da hotunan ziyarar da Osinbajo ya kai wa iyayen Hanifa a Kano
Osinbajo ya ziyarci iyayen yarinyar da ake zargin malamin makarantarsu ya kashe ta a Kano. Hoto: Tolani Alli
Asali: Twitter

Bidiyo da hotunan ziyarar da Osinbajo ya kai wa iyayen Hanifa a Kano
Hotunan ziyarar da Osinbajo ya kai wa iyayen Hanifa a Kano. Hoto: Tolani Alli
Asali: Twitter

Ga bidyon ziyarar a kasa:

Kara karanta wannan

Ka goyi bayan Tinubu: 'Yan Kudu sun nemi Osinbajo ya janye batun gaje kujerar Buhari

Kisan Hanifa: Rashin lauya da zai kare su Tanko ya janyo jinkiri a shari'ar da ake musu

Tunda farko, kun ji cewa bayan gurfanar da Abdulmalik Tanko tare da wadanda ake zargin sun hada kai don halaka Hanifa Abubakar ‘yar shekara 5, a ranar Litinin, an samu koma-baya dangane da shari’ar kasancewar wadanda ake zargin ba su da lauyan da zai kare su, Vanguard ta ruwaito.

An gurfanar da Abdulmalik tare da Hashimu Isyaku da Fatima Bashir bisa zargin su da laifuka biyar, wadanda suka hada da bayar da hadin-kai wurin yin aika-aika, garkuwa da mutane da kuma aikata kisan kai wanda laifukan sun ci karo da sashi na 97, 274, 277 da 221 na penal code.

Yayin da aka gabatar da shari’ar gaban alkali Usman Na’abba, inda ba su da lauya mai kare su, sun bukaci kotu ta roki gwamnatin Jihar Kano ta sama musu lauyan da zai kare su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel