Boka da magani: Yadda wata bokanya ke samun N1.8m a rana, ta mallaki makeken gida

Boka da magani: Yadda wata bokanya ke samun N1.8m a rana, ta mallaki makeken gida

  • Ba kamar sauran bokaye a kasar nan ba, Anna Mutheu mace ce mai arziki kuma ba ta tsoron nuna dukiyarta a kasancewarta boka
  • Bokanyar an kiyasta cewa tana samun kusan Naira miliyan 6.5 duk wata daga kudaden da masu zuwa neman sa'a a wurinta
  • Matar 'yar asalin garin Tala, gundumar Machakos, ba ta taba fashin zuwa coci ba kuma ta saka hannun jari a wasu bangarorin kasuwanci da dama

Daya daga cikin mashahuran bokaye a kasar Kenya ta fito ne daga garin Tala, gundumar Machakos kuma ana kiranta da Anna Mutheu.

Mutheu ta yi watsi da ra'ayin da ake cewa bokaye na rayuwa a cikin mawuyacin hali yayin da take gudanar da rayuwar ta kamar sarauniya.

Gidan bokanya
Boka da magani: Yadda wata bokanya ke samun N1.8m a rana, ta mallaki makeken gida | Hoto: The Nairobian
Asali: UGC

Bokanyar ta mallaki katafaren gida wanda aka yi kiyasin ya kai darajar kudi Naira miliyan 146.

Kara karanta wannan

Makashin Hanifa Abubakar: Kotu ta dage zaman hukunta AbdulMalik Tanko

A cewarta:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Yawancin mutane suna daukan cewa bokaye matalauta ne kuma suna rayuwa cikin zulumi. Ba haka lamarin yake ba. Ni mace ce mai arziki, kuma sana’ar bokanci ta sa na yi arziki."

Dukiyarta

Gidan Mutheu mai hawa daya yana da wurin ninkaya da gareji tare da manyan motoci. Hakazalika, akwai dimbin abokan harkallarta da ke neman ta yi musu bokanci, tana samun kudi mai yawa daga kasuwancinta na bokanci, in ji Standard Media.

A kiyasin ta, tana karbar abokan ciniki tsakanin 60 zuwa 80 a rana wadanda ke biyan kudin bokanci akalla N3600.

Rayuwar bokanya a gidanta
Boka da magani: Yadda wata bokanya ke samun N1.8m a rana, ta mallaki makeken gida | Hoto: The Nairobian
Asali: UGC

Samun abokan ciniki 60 a rana yana nufin Mutheu tana samun Naira miliyan 1.8 a rana. Duk da haka, mafi yawan dukiyar Mutheu ba daga bokanci ba ne sai dai daga kasuwancin da take gudanarwa.

Ta zuba jari a harkar gidaje kuma ta mallaki gidan mai, manyan motoci, da motocin hidimar jama'a. Gidanta yana yankin Malindi, Tala, Nairobi na kasar Kenya.

Kara karanta wannan

Na sanar da Atiku cewa ya tsufa kuma gajiye ya ke, ba zai iya shugabanci ba, Gwamnan Bauchi

Ya batun ibada?

Abin mamaki, Mutheu tana neman kusanci da ubangiji kuma tana zuwa coci akai-akai duk ranar Lahadi. A cewarta, Littafi Mai Tsarki yana taimaka mata sa’ad da take aikinta na bokanci.

Mutheu ta ce mahaifiyarta ce ta koya mata sana'ar bokanci, wadda ita ma bokanya ce.

A cewarta:

"Lokacin da aka haife ni, ruhun bokanci yana jikina."

Rayuwa cikin hadari

Kasancewa mai arziki haka yakan zo da matsaloli masu yawa.

A ranar 23 ga Agusta, 2020, Mutheu ta yi ikirarin rayuwarta na cikin hadari bayan da gidan rediyo ya yi ikirarin cewa ta adana sama da KSh miliyan 30 a gidanta.

Bokanyar ta yi ikirarin cewa ta samu kira daga wata lamba ta sirri kuma wasu da ba ta san ko su waye ba sun bukaci ta basu kudin.

Wannan ne gidan Mutheu
Boka da magani: Yadda wata bokanya ke samun N1.8m a rana, ta mallaki makeken gida | Hoto: The Nairobian
Asali: UGC

A farkon 2018, an kama Mutheu bayan da jami’an tsaro suka kai samame a gidanta tare da kwato katin shaidan dan kasa sama da 130.

Kara karanta wannan

Rayuwar Aure: Kotu ta datse Igiyoyin auren wata mata saboda mijin ya faɗa soyayya da kare

An kama ta ne da laifin gudanar da wata tawagar satar motoci amma daga baya aka sake ta bayan da masu gabatar da kara suka kasa gabatar da shaidun da ke alakanta ta da satar.

A wani labarin, wani mutum mai shekaru 52, Adam Muhammed, ya yanke shawarar yin tattaki daga birnin Landan zuwa Makka da kafa. Ya fara tafiya a watan Agusta 2021.

Tsawon watanni da fara tafiyar, ya kan rubuta komai da ke tafiya ta yanar gizo, inda mabiyansa suke taya shi murna da kara masa karfin gwiwa.

Mutanen da suka san inda ya sauka a kowane lokaci sukan ba shi makwanci, su ciyar da shi, kuma su taimaka masa wajen ci gaba da tafiyarsa, in ji rahoton TRT Word.

Asali: Legit.ng

Online view pixel