Da dumi: Yan bindiga sun kashe Hakimi da wasu jama'arsa a jihar Katsina

Da dumi: Yan bindiga sun kashe Hakimi da wasu jama'arsa a jihar Katsina

  • Tsagerun yan bindiga sun kai hari cikin dare karamar hukumar Jibia dake jihar Katsina ranar Alhamis
  • Akalla mutum biyar sun rasa rayukansu, cikinsu har da Hakimin garin Yangayya wanda suka kashe cikin gidansa
  • Hukumar yan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar harin da kuma adadin wadanda aka hallaka

Katsina - Yan bindiga masu garkuwa da mutane kimanin 200, sun dira garin Yangayya dake karamar hukumar Jibia a jihar Katsina cikin daren Alhamis, 3 ga watan Junairu, 2022.

Premium Times ta ruwaito cewa yan bindiga sun kashe Dagacin garin tare da mutum hudu.

Wani mazaunin Jibia, Halilu Kabir, ya bayyanawa manema labarai cewa yan bindigan sun kwashe sa'o'i uku suna cin karensu ba babbaka.

Yace:

"Sun shigo kan babura kuma suka fara harbi. Yayinda suke bi gida-gida suka kashe mutum hudu da suke kokarin guduwa."

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Masu garkuwa da mutane sun 'kwace' iyakokin jihohi 2 a Najeriya

Da dumi: Yan bindiga sun kashe Hakimi da wasu jama'arsa a jihar Katsina
Da dumi: Yan bindiga sun kashe Hakimi da wasu jama'arsa a jihar Katsina Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Wani dan garin amma mazaunin kwaryar Katsina, Ibrahim Safiyanu, yace an kashe Hakimin ne a cikin gidansa.

Yace:

"Bisa labarin da muka samu, yan bindigan sun kasheshi a gidansa. Hukumomi sun sanar da mu cewa za'a birneshi yau a Katsina."

Kakakin hukumar yan sandan jihar Gambo Isa, ya tabbatar da hari da kisan hakimin.

Sanatan APC ya koka kan yawaitar garkuwa da mutane a ƙasar

Adamu Aliero, sanata mai wakiltar Kebbi ta tsakiya ya kwatanta garkuwa da mutanen da ke ta karuwa a kasa a matsayin abin kunya ga Najeriya.

Aliero ya yi wannan maganar ne ranar Laraba yayin wani taron muhawara da Bello Mandiya, Sanata mai wakiltar Katsina ta Kudu ya shirya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace mutane 29 a wani ƙauyen Katsina, 'Yan Sanda

Mandiya ya janyo hakalin takwarorinsa a kan garkuwa da fiye da mutane 30 da ‘yan bindiga suka yi a karamar hukumar Faskari da ke Jihar Katsina.

Asali: Legit.ng

Online view pixel