Yanzu-yanzu: Kotu ta bada belin jagoran Win/Win, Muaz Magaji

Yanzu-yanzu: Kotu ta bada belin jagoran Win/Win, Muaz Magaji

  • Bayan kwanaki biyu a garkame, kotu ta baiwa tsohon kwamishanan Ganduje belin milyan daya
  • Alkali ya bayar da sharruda biyu da ya wajaba Muaz Magaji ya cika kafin a sakesa
  • Gwamna Ganduje ne ya shigar da karar Muaz Magaji kotu bisa zargin batancin da yayi masa a yanar gizo

Kano - Wata kotu a Jihar Kano ta bada belin tsohon kwamishinan ayyuka na jihar, Injiniya Mu'azu Magaji wanda aka fi sani da Dan Sarauniya Win/Win.

Kotun da ke zamanta a unguwar Nomansland ta bayar da belin ne kan naira miliyan daya, rahoton BBC.

Hakazalika an gindaya masa wasu sharuda wanda ya hada kawo mutane biyu da zasu tsaya masa.

Mutum daya ya kasance Limamin unguwa ko kwamdanda Hizbah, na biyu kuma Maigarin kauyen Muaz Magaji.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Dan Sarauniya zai ƙara kwana a gidan Yari saboda shari'ar Sheikh Abduljabbar

Muazu Magaji ya kara kwana ɗaya a gidan gyaran hali saboda ranar cigaba da shari'arsa ya ci karo da na Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.

Muaz Magaji
Yanzu-yanzu: Kotu ta bada belin jagoran Win/Win, Muaz Magaji Hoto: DailyNigerian
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kama Muaz Magaji

Wani lauya ya danganta kama tsohon Kwamishinan Ayyuka a jihar, Mu'azu Magaji, da zargin wallafa hoto na ɓata suna da ya yi a dandalin sada zumunta.

Yan sanda sun gayyaci tsohon Kwamishinan, Mu'azu Magaji, bayan karar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya shigar a kan tsohon kwamishinansa da ya sauya ya zama mai sukarsa.

Yan sanda sun tabbatar da kama shi ta bakin kakakin yan sanda Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, inda ya ce an shigar da korafi a kansa ne.

Ya ce rashin amsa gayyatar da suka dade suna yi wa tsohon Kwamishinan yasa aka kama shi.

Ganduje ya yi korafi game wallafa hotunan bata sunansa da Magaji ya yi

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban hukumar yakin rashawa a Kano, Muhuyi Rimin Gado ya shigar da Ganduje Kotu

A cikin takardar korafin da gwamnan ya aike, an shaida wa kotu cewa Magaji ya wallafa wani hoto da ke nuna wanda muke karewa (Ganduje) a matsayin mutum mara tarbiyya da tsohon Allah da ke aikata baɗala da wata mata wanda aka haska fuskar ta a hoton.

Asali: Legit.ng

Online view pixel