Sarkin Daura: Amaechi ya cancanci sarauta a masarautar mu

Sarkin Daura: Amaechi ya cancanci sarauta a masarautar mu

  • Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouq Umar, ya ce ya dace su karrama Ministan sufuri, Rotimi Amaechi a ba shi sarauta a masarautar su, a ranar 5 ga watan Fabrairu
  • Galadiman Daura kuma Dagacin Mai’Adua, Alhaji Ahmad Diddiri ya yi furucin nan a madadin Sarkin Daura a ranar Alhamis, inda ya ce Amaechi ya tallafa wa Najeriya
  • A cewarsa masarautar ba za ta karrama shi bisa wata alaka ta siyasa ko kuma wani dalili na daban banda taimakon masarautar da kasa baki-daya da ya jajirce wurin yi

Jihar Katsina - Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Farouq Umar ya ce ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya cancanci sarauta a Daura ranar Asabar, 5 ga watan Fabrairu, The Nation ta ruwaito.

Galadiman Daura kuma dagacin Mai’Adua, Alhaji Ahmad Diddiri Ahmad, ya yi wannan furucin a maimakon basaraken a ranar Alhamis, inda ya sanar da manema labarai cewa hakan ya na da alaka da taimakon da yake yi wa masarautar, Jihar Katsina da kasar baki-daya.

Kara karanta wannan

Harin Boko Haram a Buratai: Shugaban Sojoji ya ziyarci Borno, ya tattauna da Sojoji

Sarkin Daura: Amaechi ya cancanci sarauta a masarautar mu
Amaechi ya cancanci sarauta a masarautar mu, Sarkin Daura. Hoto: The Nation

Ya ce:

“Masarautar bata alakanta kanta da wata jam’iyya ba kuma za ta ba Amaechi sarautar ne saboda kokarin sa.
“Mun lura da abubuwa biyu ne na tallafin da ya yi wa masarautar Daura, Jihar Katsina da kuma kasa baki-daya.
“Duk da halin da kasa take ciki, an yi Jami’ar Sufuri a nan Daura wanda hakan zai zama babbar hanyar kawo ayyukan yi ga mutanen mu.”

Ya bayyana yadda Amaechi ya gina hanyoyin jirgin kasa da ya bi ta daura

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, ya kara da tuna yadda aka yi titina biyu na jirgin kasa da ya shiga ta Daura wanda hakan zai taimaka wa hada-hadar kasuwancin jama’a, wanda ya wuce ta Jihar Kano zuwa Niamey har Dakar wanda mutane da dama za su amfana da shi.

Kara karanta wannan

Hotuna: Jam'iyyar APC ta yi babban kamu, fitaccen sanata ya bar PDP ya shigo APC

Yayin da aka tambaye shi idan sarautar zata bayar da sarautar ne saboda matsayin Amaechi a wurin Shugaba Buhari, Galadiman Daura cewa ya yi wannan surutai ne na mutane.

A cewarsa, masarautar su bata da alakar siyasa da ko wacce jam’iyya kuma ba ta karrama wani akan dalilin siyasa.

A cewarsa da tsarkin niyya za su karrama shi

Ya ce:

“Niyya tsarkakakkiya muke da ita akan karramawar da zamu yi masa, kuma mun yaba da kokarin sa ne don haka muke shirin kara masa kwarin guiwar ci gaba da yin hakan.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel