Ba zamu taba iya hana fasa kwabri ta jihar Katsina ba: Hukumar Kwastam

Ba zamu taba iya hana fasa kwabri ta jihar Katsina ba: Hukumar Kwastam

  • Babban jami'in hukumar kwastam ya bayyana cewa hana shigowa da kaya Najeriya ta jihar Katsina ba zai yiwu ba
  • Kwantrola yace ko da hukumar Kwastam zasu zuba dukkan ma'aikatanta a Katsina, hana shigo da kaya ba zai yiwu ba
  • Sakataren gwamnatin jihar Katsina ya yi kira ga gwamnatin tarayya su bude iyakokin Najeriya kawai

Katsina - Kwantrolan hukumar Kwastam dake jihar Katsina, Wada Chedi, ya yi bayanin dalilin da yasa jami'an hukumarsa suka gaza hana fasa kwabrin haramtattun kayayyaki ta jihar.

Chedi ya bayyana cewa akwai hanyoyi da yawa da masu fasa kwabrin ke amfani da shi wajen shigo da kayayyaki.

Najeriya na iyaka da Nijar ta karamar hukumar Jibia dake jihar Katsina.

Wada Chedi ya bayyana haka a taron masu ruwa da tsaki ranar Alhamis a jihar Katsina, rahoton PremiumTimes.

Kara karanta wannan

Zargin handamar N2.9b: Ka tsawatar wa EFCC, Okorocha ga Buhari

Hukumar Kwastam
Ba zamu taba iya hana fasa kwabri ta jihar Katsina ba: Hukumar Kwastam Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Kwantrolan yace adadin jami'an kwastam dake Najeriya ba zai isa hana shigo da kaya ba.

Yace:

"Ba zai yiwu hafsoshinmu su mamaye ko ina ba ko da za'a kwaso dukkan jami'an kwastam na Najeriya, ba zamu iya tare dukkan hanyoyin shiga ba, shiyasa muke son jama'a su taimaka mana da bayanai kan masu fasa kwabri."
"Akwai hanyoyin shiga 12 a jihar Katsina amma yanzu, akwai sama da hanyoyi 100 da mutanen nan ke amfani wajen shigo da kayayyaki."

Ya kara da cewa masu fasa kwabri na da dabaru daban-daban wajen gujewa jami'an tsaro.

Jawabin gwamnatin Katsina

Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Mustapha Inuwa, ya ce rufe iyakokin Najeriya bai hana shigo da haramtattun kayayyaki ba har yanzu.

Ya yi kira ga jami'an kwastam su duba halin da al'ummar jihar ke ciki su bude iyakokin.

Kara karanta wannan

Takara a 2023: Gwamna ya ko'da kansa, ya ce shi kadai ya cancanci kujerar Buhari a 2023

Inuwa yace:

"Idan gaskiya muke son ji, rufe iyakokin bai hana fasa kwabri ba. Kuje iyakokin ku gani, mutane na shigowa da kaya. Saboda haka kawai a bude."

Jami'an Kwastam sun yi ram da manyan motoci 17 maƙare da buhunan Shinkafar kasar waje

A wani labarin kuwa, Jami'an hukumar kwastam na sashin Operation a shiyyar A, ranar Laraba, sun sanar da kwace manyan motocin dakon kaya 17 maƙare da Shinkafar waje ana kokarin shigo da ita cikin Najeriya.

Tribune Online ta rahoto cewa jami'an sun yi ram da manyam motocin dakon kayan ne a yankin Papalanto a jihar Ogun.

Da yake jawabi a wurin taron manema labarai a Legas, muƙaddashin Kwanturola na shiyyar, Hussein Ejibunu, ya bayyana yawan shinkafar da suka kwace cikin makonni biyar kacal.

Asali: Legit.ng

Online view pixel