Zargin handamar N2.9b: Ka tsawatar wa EFCC, Okorocha ga Buhari

Zargin handamar N2.9b: Ka tsawatar wa EFCC, Okorocha ga Buhari

  • Tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya yi kira ga shugaba Buhari da ya tsawatar wa da EFCC kan abinda ta ke masa
  • Okorocha ya zargi hukumar yaki da rashawan tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati da hantararsa tare da firgita shi
  • Ya ce babu shakka wannan halayyar ta son kai ce, daukar mataki kafin kotu tare da rawa da kidan wasu 'yan siyasa

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Imo, Roochas Okorocha ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya tsawatar wa hukumar yaki da rashawa, inda ya yi kira ga shugaban kasar da ya shiga tare da hana EFCC hantara da tsorata shi kan zarginsa da wawurar kudi har N2.9 biliyan.

A wata tattaunawa da manema labaran gidan gwamnati bayan ziyarar shugaban kasan da yayi, Sanata Okorocha ya yi bayanin cewa, akwai hukuncin kotu da wasu umarni biyu daga wasu kotu kan cewa hukumar ta kyale shi.

Kara karanta wannan

An tura matashi zaman gidan yarin shekara kan laifin zambar N15.4m a Maiduguri

Zargin handamar N2.9b: Ka tsawatar wa EFCC, Okorocha ga Buhari
Zargin handamar N2.9b: Ka tsawatar wa EFCC, Okorocha ga Buhari. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

Ya koka kan yadda wadannan umarnin na kotu suka shiga ta kunne na hagu suka fice ta kunnen dama na hukumar yaki da rashawan.

Okorochan ya kwatanta wannan abun da EFCC ke yi da son kai, aiwatar da hukunci kafin kotu kuma 'yan siyasa ne suke zuga su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tsohon gwamnan ya yi kira ga shugaban kasan matsayinsa na wanda ke tsayuwa kan doka da ya yi magana kan lamarin.

Gwamna Okorocha ya kara da bayyana bukatar kara karfafa jam'iyyar mai mulki tun daga tushen ta, Channels TV ta ruwaito.

Kamar yadda yace, shugaban ya jaddada cewa, 'yan siyasan da ke hayewa madafun iko daga Abuja, ba tare da soyayya ko yardar talakawa ba daga tushe, ba za a sake aminta da su a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ba.

Kara karanta wannan

Buhari ba zai iya tafiyar mota babu shiri ba, Fadar shugaban kasa ta yi wa PDP martani kan ziyarar Zamfara

EFCC ta damke tsohon gwamna, Rochas Okorocha, a Abuja

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya shiga hannun hukumar yaki da rashawa da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, jaridar Premium Times ta tabbatar.

Jami'an hukumar EFCC sun kama Okorocha wurin karfe 4 na yammacin Talata a ofishinsa dake Abuja, majiya ta tabbatar.

Majiyar da ta tabbatar, ta ce hukumar ta dinga tura gayyata ga tsohon gwamnan zuwa ofishinta dake Abuja saboda harkallar wasu kudade amma ya ki zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel