Tashin Hankali: Halin da ake ciki kan batun ɗan uwan Goodluck Jonathan da yan bindiga suka sace

Tashin Hankali: Halin da ake ciki kan batun ɗan uwan Goodluck Jonathan da yan bindiga suka sace

  • A watan da ya gabata ne wasu miyagun yan bindiga suka yi garkuwa da ɗan uwan tsohon shugaban ƙasa, Jonathan a Bayelsa
  • Sama da mako ɗaya da faruwar lamarin, wata majiya daga cikin iyalansa ta shaida cewa har yanzun maharan ba su tuntuɓe su ba
  • Kakakin hukumar yan sandan jihar Bayelsa ya tabbatar da cewa jami'ai na cigaba da kokarin ceto shi da kame maharan

Bayelsa - Sama da mako ɗaya kenan da yin garkuwa da ɗan uwan tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, amma har yanzun ba amo ba labari.

Daily Trsut ta rahoto cewa a ranar Litinin 24 ga watan Janairu, 2022, wasu tsagerun yan bindiga suka yi awon gaba da Jephthah Robert Yekorogha, a Yenagoa, jihar Bayelsa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Miyagu sun kashe mataimakin kwamishinan yan sanda

Taswirar jihar Bayelsa
Tashin Hankal: Halin da ake cikin kan batun ɗan uwan Goodluck Jonathan da yan bindiga suka sace Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Sai dai tun bayan wannan lokaci, waɗan da suka yi garkuwa da fitaccen ɗan siyasan kuma ɗan uwan Jonathan ba su sako shi ba.

Wata majiya daga cikin iyalan wanda aka yi garkuwa da shi, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida mana cewa har zuwa yanzun masu garkuwan ba su tuntuɓe su ba.

Ƙanin wanda aka yi garkuwa da shi, kuma wanda ya kafa kamfanin Zeetin Engineering Company, Mista Aziboala Robert, ya tabbatar da garkuwa da yayansa a wata sanarwa da ya fitar.

Amma a cewarsa, tun bayan aukuwar lamarin, jami'an tsaro sun maida hankali wajen tabbatar da an kubutar da shi lami lafiya.

Wane mataki yan sanda ke ɗauka?

Yayin da muka tuntuɓi kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, ya tabbatar da cewa yan sanda na kokari kan lamarin.

Kara karanta wannan

Mutane zasu ga gagarumin canji a Arewa maso gabas kwanan nan, Shugaba Buhari ya tabbatar

Kakakin yan sandan yace:

"Jami'an hukumar yan sanda na kan bincike a lamarin domin kubutar da wanda aka yi garkuwa da shi da kuma kama masu hannu a kitsa lamarin."

A wani labarin na daban kuma Miyagun yan ƙungiyar asiri sun kashe mataimakin kwamishinan yan sanda

Bayanan da muka samu sun nuna cewa mambobin ƙungiyar asirin sun farmaki ACP ɗin ne a gidansa ranar Laraba, suka masa kisan gilla.

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Imo ya tabbatar da cewa ya ji labarin amma bai samu bayani a hukumance daga DPO na yankin ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel