Tinubu ganawa da wasu yaje yi Landan, ba jinya ba: Hadiminsa ya bayyana ranar da zai dawo

Tinubu ganawa da wasu yaje yi Landan, ba jinya ba: Hadiminsa ya bayyana ranar da zai dawo

Legas - Jagoran All Progressives Congress APC, Bola Tinubu, na cikin koshin lafiya kuma ba rashin lafiya yake ba, mai magana da yawunsa, Tunde Rahman, ya bayyana.

Rahaman ya tabbatar da cewa tsohon gwamnan jihar Legas ya tafi kasar waje ne doomin ganawa da wasu abokan huldan sa game da takarar kujeran shugaban kasan da yake niyyar yi a 2023.

Tinubu ganawa da wasu yaje yi Landan, ba jinya ba: Hadiminsa ya bayyana ranar da zai dawo
Tinubu ganawa da wasu yaje yi Landan, ba jinya ba: Hadiminsa ya bayyana ranar da zai dawo

Hadimin ya bayyana hakan ne a sakon SMS da ya turawa jaridar Punch ranar Juma'a.

Yace:

"Asiwaju bai tafi UK don hutu ko rashin lafiya ba. A can yake ganawa da wasu kan abubuwa masu muhimmanci."

Kara karanta wannan

Tun bayan zaben 2019 Atiku ya gudu Dubai, sai yanzu ya dawo lokacin da zabe ya gabato: Jigon PDP

"A gida ko a waje, Asiwaju na aiki koda yaushe. Yawancin mutane ba zasu iya aikin da yake ba. Hakan na nufin yana da karfi da jini sosai."
"Asiwaju zia dawo Najeriya makon gobe idan ya kammala abubuwa da yake a kasar waje."

Asali: Legit.ng

Online view pixel