Tun bayan zaben 2019 Atiku ya gudu Dubai, sai yanzu ya dawo lokacin da zabe ya gabato: Jigon PDP

Tun bayan zaben 2019 Atiku ya gudu Dubai, sai yanzu ya dawo lokacin da zabe ya gabato: Jigon PDP

  • Jigon jam'iyyar PDP ya yi kira ga Alhaji Atiku Abubakar yayi zamansa wannan karon kada ya fito takara
  • Kassim Afegbua wanda da shi akayi yakin neman zaben Atiku a 2019 yace yanzu ya dawo daga rakiyarsa
  • A cewarsa, tun bayan zaben 2019 Atiku ya gudu Dubai ya barsu a Najeriya maimakon ya zauna da jama'a

Wani jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), kuma tsohon kakakin yakin neman zaben Atku, Mr Kassim Afegbua, ya bayyana cewa basa son Atiku Abubakar yayi takara.

Afegbua ya yi kira ga uwar jam'iyyar PDP ta sauya salon siyasa yayinda ake shirin zaben 2023.

Ya bayyana hakan ne a hirar da yayi a shirin Politics Today na tashar ChannelsTV.

Kara karanta wannan

Atiku shekaru 4 kadai zai yi idan ya hau mulki, Shugaban kwamitin yakin zabensa

Jigon PDP
Tun bayan zaben 2019 Atiku ya gudu Dubai, sai yanzu ya dawo lokacin da zabe ya gabato: Jigon PDP Hoto
Asali: Facebook

Afegbua yace tun 1990 Alhaji Atiku Abubakar yake takaran neman kujeran shugaban kasa har yanzu, saboda haka ya huta ya bari masu sabbin jini suyi.

Yace:

"Maganata na kan wani dan takara wanda ya wakilci jam'iyyarmu a zaben 2019. Na fada na sake, mun gaji da ganin tsaffin fuskoki."
"Daga 1990 zuwa 2019, Alhaji Atiku Abubakar, ya kasance yana takarar kujerar shugaban kasa."
"Ya bar mu a Najeriya ya koma Dubai tsawon shekaru biyu da rabi, babu wani janar din Soja da za kai yaransa faggen yaki kuma ya gudu ya barsu bayan an fadi a yakin."

Asali: Legit.ng

Online view pixel