Buhari ya aike wa Zamfarawa sakon bidiyo da na rediyo kan fasa ziyararsu da ya yi

Buhari ya aike wa Zamfarawa sakon bidiyo da na rediyo kan fasa ziyararsu da ya yi

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika sakon bidiyo da na rediyo ga Zamfarawa kan fasa ziyartar su da yayi a ranar Alhamis
  • Ya mika jajen sa ga jama'ar Zamfara kan rashin yanayi mai kyau da ya hana jirgin sa mai tashin ungulu iya tashi daga Sokoto zuwa Gusau
  • Ya yi fatan samun yanayi mai kyau nan gaba tare da mika godiyar sa ga Gwamna Bello Matawalle na jihar kan kokarin ganin ziyarar ta tabbata

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike da sakon bidiyo da na rediyo ga jama'ar jihar Zamfara bayan ya soke ziyartar su da ya yi niyya a ranar Alhamis sakamakon matsalar yanayin gari.

Vanguard ta ruwaito cewa, a sakon shugaban kasan, ya ce:

Buhari ya aike wa Zamfarawa sakon bidiyo da na rediyo kan fasa ziyararsu da ya yi
Buhari ya aike wa Zamfarawa sakon bidiyo da na rediyo kan fasa ziyararsu da ya yi. Hoto daga vanguardngr.com
Asali: UGC

"Ya ku jama'a ta na jihar Zamfara. Na matukar jin kuna ta yadda na kasa kasancewa da ku a yau kamar yadda na tsara. Na kammala abinda na zo yi a Sokoto a kamfanin siminti na BUA kuma na shirya tsaf domin ganin ku.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta yi nasara a gwagwaryar da take da matsalolin tsaro, Buhari ya ba da tabbaci

“An sanar da ni cewa ba zan iya tafiyar ba saboda yanayin gari maras kyau wanda ya sa jirgi na mai saukar ungulu ba zai iya zuwa Gusau daga Sokoto ba."

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, ya kara da cewa:

“Na fahimci yadda ku ke ji a kan wannan cigaban amma na san cewa za ku yadda da ni cewa Allah ne masanin komai. Ina matukar jajanta wa Gwamnan ku, Bello Matawalle, da kuma tawagar sa wadanda suka shirya komai tsaf domin ganin nasarar ziyarar.
"Ina fatan samun yanayi mai kyau nan gaba idan zan kawo muku ziyara.
“Ina umartar hukumomin tsaro da su cigaba da addabar 'yan ta'adda, sun kiyaye shigowar baki ta iyakokin kasar nan tare da hana zuwa wurin hako zinari ba bisa ka'ida ba a jihar.

Kara karanta wannan

2023: Zan kawar da karuwai idan nayi nasara a zabe, Dan takaran shugaban kasa yayi alkawari

"Gwamnatin tarayya da ta jihar Zamfara suna aiki wurin tabbatar da zaman lafiya ya dawo dukkan sassan jihar cikin kankanin lokaci kuma muna tsammanin 'yan jihar za su bayar da hadin kai da goyon baya ta kowanne fanni.
"Allah ya yi wa jama'ar Zamfara albarka."

Tun da an ki yarda a kara farashin mai, zamu cigaba da cin bashi kenan: Fadar Shugaban kasa

A wani labari na daban, Najeriya zata ciyo basussukan kudi sakamakon dakatad da shirin kara farashin man fetur ta hanyar cire tallafin mai, fadar shugaban kasa ta bayyana ranar Laraba.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana hakan a hirar da yayi a tashar ChannelsTV.

A cewarsa, ko yan Najeriya sun so ko sun ki, dole a nemo kudi ta wani hanya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel