Zan murƙushe yan ta'adda baki ɗaya kafin na sauka daga mulki, Shugaba Buhari

Zan murƙushe yan ta'adda baki ɗaya kafin na sauka daga mulki, Shugaba Buhari

  • Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ce kafin ya miƙa mulki a 2023, sai ya ga bayan yan ta'adda baki ɗaya, zaman lafiya ya dawo
  • Buhari wanda ya kai ziyara fadar Sarkin Musulmi a Sokoto, yace abun damuwa ne matauƙa yadda mutanen dake rayuwa tare, suke kashe junan su
  • Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya gode wa shugaban bisa samun lokaci har ya kawo masa ziyara fadarsa

Sokoto - Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya tabbatarwa yan Najeriya cewa gwamnatinsa zata kawo ƙarshen ayyukan yan bindiga da ƙalubalen tsaro kafin wa'adinsa ya ƙare a 2023.

Buhari ya yi wannan furucin ne a fadar mai martaba Sarkin Musulmi dake Sokoto ranar Alhamis, yayin da ya kai masa ziyara, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Buhari: Lamarin tsaro a arewa maso yamma yana matuƙar damu na

Shugaba Buhari, Sultan da gwamna Tambuwal
Zan murƙushe yan ta'adda baki ɗaya kafin na sauka daga mulki, Shugaba Buhari Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Shugaban ƙasan ya nuna tsantsar damuwarsa game da halin da mutane ke ciki a arewa maso yamma, inda ya ce baya iya runtsawa ya yi bacci.

Buhari yace:

"Abun damuwa ne matuƙa, al'umma ɗaya da al'ada iri ɗaya amma suna kashe junan su ba tare da wani kwakkwaran dalili ba."

Shugaban ƙasa ya kuma tabbatar da cewa zai miƙa mulkin Najeriya bayan ya murkushe duk wata damuwa ta rashin tsaro da faɗuwar tattalin arziki.

Zamu cigaba da addu'a - Sultan

Da yake nasa jawabin, mai martaba sarkin musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya ce a matsayin shugabannin addini, za su cigaba yi wa Najeeiya Addu'a.

Mai Martaba Sarkin yace ba za su gajiya ba wajen yi wa ƙasar nan Addu'ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali mai ɗore wa.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari zai miƙa mulki ga ɗan takarar APC a 2023 Insha Allahu, Garba Shehu ya magantu

Sarkin ya nuna jin daɗinsa tare da miƙa godiyarsa ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, bisa samun lokaci ya kawo masa ziyara har Masarautarsa.

A wani labarin kuma Hukumar yan sandan ƙasar na ta yi martani kan hatsarin da Jirgin ta mai saukar Angulo ya yi a Bauchi

Hukumar yan sandan ƙasar nan ta musanta rahoton da ake yaɗa wa cewa jirgin ta ya yi hatsari a Bauchi har wasu mutane sun jikkata.

Kakakin hukumar na ƙasa, Frank Mba, yace jirgin ya taso daga Abuja kuma ya isa Bauchi da safiyar Alhamis, ya sauka lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel