Cikin jihohi 36, An bayyana gwamnan jihar da ya fi kaunar zaman lafiya a Najeriya

Cikin jihohi 36, An bayyana gwamnan jihar da ya fi kaunar zaman lafiya a Najeriya

  • Gidauniyar wanzar da zaman lafiya ta baiwa gwamnan jihar Enugu, lambar yabo ta gwamnan da ya fi son zaman lafiya a Najeriya
  • Shugaban gidauniyar, Dakta Sulaiman Adejoh, yace sun yi nazari kan muhimman ayyukan gwamnan kafin su zaɓe shi
  • Da yake godiya kan girmamawar da aka masa, gwamnan ya sadaukar da nasarar da ya samu ga Allah

Enugu - Gwamnan jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi, ya samu lambar yabo ta ƙasa, "Gwamnan da ya fi son wanzar da zaman lafiya a Najeriya," kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Gidauniyar wanzar da zaman lafiya, (Messengers of Peace Foundation) ita ce ta baiwa gwamnan wannan lambar yabo ta ƙasa.

Ifeanyi Ugwuanyi
Cikin jihohi 36, An bayyana gwamnan jihar da ya fi kaunar zaman lafiya a Najeriya Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Da yake miƙa kyautar ga gwamnan a fadar gwamnatin jihar Enugu, shugaban gidauniyar, Dakta Sulaiman Adejoh, ya ce sun zaɓi gwamnan ne duba da namijin kokarinsa wajen wanzar da zaman lafiya a Enugu.

Kara karanta wannan

Bayan dage ziyarar Zamfara, Buhari ya shirya zuwa jihar Nasarawa wata mai kamawa

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Akwai zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Enugu da ƙasa baki ɗaya. Mun duba kokarinsa saboda ba kasafai ake samun mutane kamarsa ba."
"Mutumin da zai amfani da duk wata dama, har da wacce ke tsakaninsa da Allah, wajen tabbatar da mutane sun samu kwanciyar hankali a jiha."
"Kuma da karfin ikon da kake da shi a matsayin gwamnan Enugu, ka yi amfani da wannan iko wajen sanya kwanciyar hankali a zuƙatan al'umma."

Dakta Adejoh ya shaida wa gwamnan cewa sun zo ne domin miƙa masa lambar yabo ta gwamnan zaman lafiya bayan dogon nazari da kuma duba yanayin jiharsa.

"Mun zagaye jihar Enugu musamman yankunan karkara, mun ga hanyoyi masu kyau. Zamu tura maka Bidiyo ka ji yadda mutane ke yaba maka."

Babu abin da zai tafi sai da zaman lafiya

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban kasa ta tonawa Gwamnan PDP asiri, ta ce ya fi kowa rashin biyan albashi

Da yake nasa jawabin, gwamna Ugwuanyi, ya ce ya sadaukar da kyautar ga Allah, domin a cewarsa Shi ke taimaka masa har ya samu waɗan nan nasarori.

Ya ce gwamnati ba zata samu nasara kan muhimman kudurinta ga al'umma, tsaro da walwala, ba tare da kwanciyar hankali ba.

A wani labarin na daban kuma Shugaba Buhari ya kuduri aniyar murkushe yan bindiga baki ɗaya kafin wa'adinsa ya ƙare a 2023

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya ce kafin ya miƙa mulki a 2023, sai ya ga bayan yan ta'adda baki ɗaya, zaman lafiya ya dawo.

Buhari wanda ya kai ziyara fadar Sarkin Musulmi a Sokoto, yace abun damuwa ne matauƙa yadda mutanen dake rayuwa tare, suke kashe junan su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel