Bayan shekaru 37 a Kurkuku, an saki mutumi bayan an gano karya akayi masa

Bayan shekaru 37 a Kurkuku, an saki mutumi bayan an gano karya akayi masa

  • Kotu ta saki wani mutumin da aka jefa kurkuku shekaru 37 da suka wuce kan laifin da bai aikata ba
  • Wanda ya bada shaida a kotu ne ya dawo saboda nadama ya tona asirin kansa
  • Willie ya ce shi yanzu babu matsala, ya yafewa kowa kuma yana farin cikin zai cigaba da rayuwarsa

Pennsylvania - Wani mutumi a kasar Amurka ya samu yanci bayan shekaru 37 a kurkuku yayinda aka gano karyar laifin kisan kai akayi masa a shekarar 1984 a birnin Philadelphia.

Mutumin mai suna, Willie Stokes, wanda aka saki a watan Junairu 2022 ya shigar gwamnatin kotu kan zaluncin da aka masa.

Associated Press ta ruwaito cewa mutumin da ya bada shaida a kotu a kansa a 1984 ya bayyana cewa kwayoyi da yan mata akayi masa alkawari ya yiwa Willie Stokes sharri.

Kara karanta wannan

Tattaki: Yadda bature ya taso daga Landan zuwa Makka da kafa, ya fadi manufarsa

Willie Stokes yace:

"Komai ya wuce. Ina farin ciki zan cigaba da rayuwata."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan shekaru 37 a Kurkuku, an saki mutumi bayan an gano karya akayi masa
Bayan shekaru 37 a Kurkuku, an saki mutumi bayan an gano karya akayi masa Hoto: Matt Rourke/AP Photo
Asali: Facebook

Sama da mutane 100 aka saki kawo yanzu a jihar Pennsylvania dake Amurka bayan sun kwashe shekaru a kurkuku, Diraktan ceto masu gaskiya a jihar Pennsylvania, Marissa Boyers Bluestine, ta bayyana.

Mutumin da yayi shaida shekaru 37 da suka gabata mai suna Franklin Lee, yace daga baya ya yi nadamar sharrin da yayi masa.

Sai Lauyoyin gwamnati suka hukuntashi kan karya da sharri kuma shima aka jefashi kurkuku.

Mutane sun tarawa mutumin da ya kwashe shekaru 43 cikin kurkuku kudi, N95m, bayan an gano sharri akayi masa

A baya mun kawo cewa an saki wani mutumi mai suna Kevin Strickland a kasar Amurka da ya kwashe shekaru 43 cikin gidan yari kan laifin da ba shi ya aikata ba.

Kara karanta wannan

Na gwammaci yashe teku: Cece-kuce yayin da budurwa ta rokon saurayi ya aureta

Kevin Strickland wanda dan garin Missouri ne a Amurka, ya shaki kamshin yanci ranar Talata, 23 ga Nuwamba, 2021.

Alkali James Welsh ya wanke mutumin daga laifukan da ake zarginsa da su na kisan mutum uku.

A shekarar 1979, an yanke masa hukuncin daurin shekaru 50.

Asali: Legit.ng

Online view pixel