Kotu ta yanke wa mahaifi ɗaurin rai-da-rai saboda ɗirka wa ƴar cikinsa ciki

Kotu ta yanke wa mahaifi ɗaurin rai-da-rai saboda ɗirka wa ƴar cikinsa ciki

  • Wata kotu da ke zamanta a Legas ta yanke wa wani Ekpo Lawrence hukuncin daurin rai dai rai ba tare da zabin tara ba saboda yi wa yarsa ciki
  • Alkalin kotun ta ce abin da mahaifin ya aikata yana da matukar muni kuma abin kunya ne don haka ya zama dole ya fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada
  • Yarinyar, mai shekaru 15 ta fada wa wata ma'aikaciya ne a makarantarsu abin da mahaifin ke mata idan matarsa ba ta gida hakan yasa aka sanar da hukuma

Jihar Legas - An yanke wa wani mahaifi mai shekaru 42, Ekpo Lawrence hukuncin daurin rai dai rai ba tare da zabin tara ba saboda yi wa yar cikinsa mai shekaru 15 ciki, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yadda jami'an EFCC suka je har kotu domin cafke wanda ake zargi a Legas

Da ta ke yanke hukuncin, Mai shari'a Abiola Soladoye, ta ce masu shigar da kara sun gabatar da gamsassun hujjoji akan tuhumar da ake yi wa Lawrence.

Kotu ta yanke wa mahaifi ɗaurin rai-da-rai saboda ɗirka wa ƴar cikinsa ciki
An yanke wa magidancin da ya yi wa yarsa ciki daurin rai-da-rai a Legas. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Saladoya, ya lura da cewa musanta aikata laifin da Lawrence ya yi wani yunkuri ne na yi wa kotu karya da wasa da hankalin shari'a, The Nation ta ruwaito.

Ta ce:

"Halin rashin da'a da wanda ake zargin ya nuna abu ne mai kazanta, muni kuma ba za a iya yafe wa ba a karkashin sashi na 137 na dokar masu laifi na Jihar Legas ta 2015 kuma abin Allah wadai ne.
"Lalata da yar cikin mutum abu ne mai matukar muni, abin kunya kuma ya saba wa al'ada da tsarin rayuwa. Abu ne wanda tarbiyya bai yarda da shi ba.

Kara karanta wannan

Tattaki: Yadda bature ya taso daga Landan zuwa Makka da kafa, ya fadi manufarsa

"Wannan babban abin ki ne don haka sai ya fuskanci hukunci bisa aikata wannan mumunan abin. Saboda wannan dalilan da na lissafa, an yanke wa wanda ake zargi hukuncin daurin rai da rai ba tare da tara ba."

Yadda lamarin ya faru

NAN ta rahoto cewa masu shigar da karar karkashin jagorancin Mrs Bola Akinsete, sun ce Lawrence ya aikata laifin ne tsakanin Disamban 2018 da Yunin 2019 a gidansa a Agege, Legas.

Wacce abin ya faru da ita, mai shekaru 15, a yayin da ya bada shaida a kotu ta ce mahaifina a lokuta da dama ya rike haike mata duk lokacin da kishiyan mahaifiyarta bata nan.

Ta ce an gano wannan abin munin ne a lokacin da yarinyar ta fada wa wata ma'aikaciya a makarantarsu abin da mahaifinta ke mata.

Lawrence, a yayin da ya ke kare kansa ya musanta yin lalata da yarsa kuma ya yi ikirarin cewa yana wurin aiki a lokacin da aka ce abin ya faru.

Kara karanta wannan

Bidiyon matashin da ya hargitsa banki, ya kwace kadarar su kan kwashe masa kudi daga asusun sa

Banbaraƙwai: Soyayya mu ke yi, yarinyar da mahaifinta ya ɗirka wa ciki a Bayelsa

A wani labarin, wata yarinya mai shekaru 14, wacce ke ajin karamar sakandare na 3, da mahaifinta ya yi wa ciki ta shaida wa yan sanda cewa soyayya suke yi, Vanguard ta ruwaito.

Yan sanda sun kama mahaifin, Baridap Needman, a Yenizue-Gene a Yenagoa, babban birnin jihar bayan wata kungiyar kare hakkin mata, GRIT, karkashin jagorancin Dise Ogbise ta yi korafi.

A cewar Dise Ogbise da Mrs Mary Accrah Pekeowei, wani makwabcin wanda abin ya faru da ita ne ya tsegunta musu bayan ya gano yarinyar na dauke da juna biyu na watanni biyar kuma mahaifinta ne ya yi cikin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel