Bidiyon matashin da ya hargitsa banki, ya kwace kadarar su kan kwashe masa kudi daga asusun sa

Bidiyon matashin da ya hargitsa banki, ya kwace kadarar su kan kwashe masa kudi daga asusun sa

  • An samu hargitsi tare da tashin hankali a wani banki da ke yankin Ikotun da ke Legas bayan da wani fusataccen kwastoma ya je huce fushin sa
  • Dan Najeriyan ya kwace wata kadarar banki yayin da ya dinga dakawa ma'aikatan tsawa kan yadda aka wawure masa kudi daga asusun bankinsa
  • Fusataccen mutumin ya nada abinda ke faruwa inda kai tsaye ya saka a Instagram tare da korafinsa duk da rokon da wata ma'aikaciya mace ke masa

Wani dan Najeriya ya janyo cece-kuce a wani banki da ke Ikotun a jihar Legas inda ya je korafi kan yadda aka washe masa kudi daga asusun bankin sa ba tare da wani dalili ba.

A wani bidiyon al'amarin da @Instablog9ja ta wallafa a Instagram, an ga mutumin ya kwace wata na'urar bankin inda ya ke barazanar fasa ta.

Kara karanta wannan

Na gwammaci yashe teku: Cece-kuce yayin da budurwa ta rokon saurayi ya aureta

Bidiyon matashin da ya hargitsa banki, ya kwace kadarar su kan kwashe masa kudi daga asusun sa
Bidiyon matashin da ya hargitsa banki, ya kwace kadarar su kan kwashe masa kudi daga asusun sa. Hoto daga @IInstablog
Asali: Instagram

Ya ki kwantar da hankalin sa

Mutumin daga nan ya fara nadar lamarin inda kai tsaye ya saka a Instagram, lamarin da yasa wata ma'aikaciyar bankin mace ta yi kokarin hanawa amma hakan bai samu ba saboda fushin da kwastoman ya shiga.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yayin da ya ke fada tare da masifa da dukkan karfin sa, ya nemi masge ma'aikaciyar da ta yi yunkurin hana shi nadar lamarin.

Kamar yadda mutumin ya ce, ya dade ya na zuwa bankin, kusan kullum na tsawon wata daya kuma har lokacin ba su dawo masa da kudin sa ba.

A yayin da ma'aikatan bankin suka cigaba da zuwa, mutumin ya yi barazanar barin bankin da na'urar da ya dauka.

Bidiyon dan sanda ya na cin zarafin wata mata, ya na barazanar harbe ta

Kara karanta wannan

Dan Allah ku taya ni da addu’ar samun lafiya, Olisa Metuh ya roki ‘yan Najeriya

A wani labari na daban, rundunar ‘yan sanda ta ce ta kama dan sanda da ya ci zarafin wata mata a wani bidiyo wanda ya yadu a kafafen sada zumunta.

A bidiyon, wanda ya yi yawa a ranar Juma’a, an ga wani dan sanda rike da bindiga ya na cin zarafin wata mata yayin da yake harbi don ya tsoratar da ita, TheCable ta ruwaito.

“Kina hauka ne, ni tsaran ki ne, sai na kashe ki,” kamar yadda aka ji dan sandan ya na fadi da turanci yayin da ya ke kokarin marin matar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel